'Yan Bindiga Sun Sako Wata Tsohuwa Mai Shekaru 90 da Suka Sace a Jirgin Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sako Wata Tsohuwa Mai Shekaru 90 da Suka Sace a Jirgin Kaduna

  • Bayan shafe kwanaki 144 a hannun'yan bindiga, karin mutum hudu sun samu 'yanci daga mafakar tsageru
  • A watan Maris din 2022 ne wasu 'yan bindiga suka farmaki wani jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Abuja
  • 'Yan Najeriya da dama sun shiga damuwa bayan samun labarin yadda aka sace mutane a mummunan harin

Jihar Kaduna - Wata tsohuwa mai shekaru 90, Halimatu Atta da aka sace a harin jirgin kasan Kaduna a watan Maris ta kubuta daga hannun 'yan bindiga.

A cewar Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald, Halima ta samu 'yanci ne tare da diyarta da kuma karin wasu mutane biyu.

An sako mata mai shekaru 90 da aka sace a jirgin Kaduna
'Yan bindiga sun sako wata tsohuwa mai shekaru 90 da suka sace a jirgin Kaduna | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewasa:

"Ina mai tabbatar da cewa a safiyar ranar Juma'a, 'yan bindiga sun sako wasu mutane hudu da suka sace a harin jirgin kasa."

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga Mama Halima, akwai kuma diyarta matar aure mai shekaru 53, Adama Atta Aliyu.

A baya an ga bidiyon Adama tana musayar yawu da 'yan bindigan da suka sace su tare da nuna fushinta da kin sakinsu da tsagerun suka yi.

Sauran wadanda aka sako sun hada da Mohammed Sani Abdulmaji (M.S Ustaz) da Alhaji Modin Modi Bodinga, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dan Halima Halima, Farfesa Abdulazeez Yusuf Atta ya tabbatar da sakin mahaifiyar tasa a wani rubutun ya yi a shafinsa na Facebook.

A cewar Farfesa:

"Ya Salaam!!! Bayan shafe kwanaki 144 a tsare, mahaifiyarmu da 'yar'uwarmu sun kubuta daga tsare su da aka yi. Muna matukar godiya da duk wani goyon baya da kuka ba mu. Mun gode."

Wasu ’Yan Bindiga Sun Bi Har Gida, Sun Hallaka Wani Lauya a Zamfara

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga

A wani labarin, wasu miygun 'yan bindiga sun bindige lauya a birnin Gusau na jihar Zamfara a ranar Alhamis din da ta gabata.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun shiga gidan Barista Benedict Azza da ke unguwar Saminaka, a Gusau, inda suka yi yunkurin sace shi.

Majiya ta bayyana cewa, an lauyan ya yi gwagwarmayar shiga motarsa da nufin ya tsere, amma 'yan bindiga suka harbe shi har sau uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel