Hotuna da bidiyo: Tinubu, Ganduje da Wasu Kusoshin Gwamnati Sun Halarci Liyafar Auren Diyar Bagudu

Hotuna da bidiyo: Tinubu, Ganduje da Wasu Kusoshin Gwamnati Sun Halarci Liyafar Auren Diyar Bagudu

  • Manyan 'yan siyasa tare da kusoshin gwamnati a kasar nan sun samu halartar gagarumar liyafar cin abincin dare ta auren diyar Atiku Bagudu
  • Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima, Gwamna Ganduje, Gwamna Bello Matawalle, Dolapo Osinbajo duk sun halarci wurin
  • Amarya tare da angonta sun sha kyau inda suka dinga shiga kayan alfarma suna walkiya tare da haske wurin liyafar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A daren Alhamis ne aka yi gagarumar liyafar cin abincin dare daga cikin shagalin murnar auren diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Maryam Bagudu da angonta Ibrahim.

Manyan 'yan siyasa, kusoshin gwamnati da gwamnoni duk sun samu halartar wurin liyafar cin abincin dare baya ga manyan mata masu ji da kansu da suka je wurin.

Kusoshin Gwamnati
Hotuna da bidiyo: Tinubu, Ganduje da Wasu Kusoshin Gwamnati Sun Halarci Liyafar Auren Diyar Bagudu. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Daga cikin bidiyon da Legit.ng ta tattaro muku, akwai wanda aka ga shigowar 'dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, suna dagawa jama'a hannu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi

Baya ga hakan, an ga bidiyon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano inda suke tsaye zasu dauka hoto tare da amaryar da mahaifiyarta da kuma Bola Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a nan aka tsaya ba, duk dai a bidiyon, an ga Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle a wurin kayatacciyar liyafar auren.

Har ila yau, matar mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, Dolapo Osinbajo ta samu halartar liyafar kuma ta dauka ido.

Amarya ta dinga shiga ta alfarma har kala biyu a wurin liyafar inda ta fito shar ta dinga walkiya gwanin birgewa da daukar ido.

Hotuna da Bidiyon kyawawan 'ya'ya matan Yariman Bakura a Shagalin Auren 'Dan uwansu

A wani labari na daban, kyawawan hotunan 'ya'ya matan Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura sun matukar birge jama'a a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawar Diyar Gwamna Atiku Bagudu

Kamar yadda fashionseriesng ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga zuka-zukan 'yan matan hudu jere reras gwani sha'awa.

Suna sanye da kaya masu kusan launi daya yayin da suka sha kwalliya irin ta zamani mai matukar birgewa da aji irin na 'ya'yan masu hannu da shuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel