Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi

Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi

  • Bidiyon matar gwamnan jihar Kebbi, Aisha Atiku Bagudu, tare da diyarta amarya Maryam Bagudu suna rausayawa a wurin liyafar auren Maryam din ya kayatar
  • A bidiyon, mahaifiyar amarya ta yi shigar alfarma kuma ta kamala da kaya masu launin sararin samaniya, lamarin da ya kara bayyana kyanta
  • Ita kuwa amarya Maryam Bagudu ta yi shiga da launin ruwan madara inda tayi caras cikin riga da mayafi irin na amaren zamani kuma suka dinga cashewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A cikin makon nan ne ake ta shagalin bikin auren diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Maryarm Atiku Bagudu.

Babu shakka bikin ya dauka kala kuma amarya ta dinga shiga ta alfarma irin ta amaren zamani kuma 'ya'yan masu hannu da shuni.

Matar Gwamna da diyarta
Bidiyo: Yadda Matar Gwamna da Diyarsa Suka Kwashi Rawa wurin Liyafar Aure, An yi Musu Ruwan Kudi. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

A daren jiya ne aka yi wata gagarumar liyafar cin abincin dare duk daga cikin shagalin auren Maryam Bagudu da angonta Ibrahim.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Tinubu, Ganduje da Wasu Kusoshin Gwamnati Sun Halarci Liyafar Auren Diyar Bagudu

Daga cikin bidiyoyin wurin liyafar, bidiyon da matar Gwamna Aisha Atiku Bagudu ta fito tare da diyarta Maryam suna cashewa inda ake ruwan kudi ya ja hankali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon, mahaifiyar amaryar ta yi shiga ta kamala inda ta sanya doguwar riga tare da rufe kanta rijif kamar yadda ta saba yi a sauran shigarta.

Kayan mahaifiyar amaryar kalar sararin samaiya ne, kalar da ta matukar dacewa da tsarinta tare da fatar jikinta.

A bidiyon casun wanda fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, amaryar ta saka kaya masu launin ruwan madara inda ta saka wani mayafi mai jan kasa wanda babu shakka ya shiga da irin yanayin tsarin amaryar.

Manyan hamshakan mata masu fadi a ji a kasar nan sun kawata wurin liyafar da irin shigarsu ta alfarma kuma an ci,an sha tare da rakashewa.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawar Diyar Gwamna Atiku Bagudu

Bidiyo da hotunan iyalan Sule Lamido a auren Surayya da Angonta Yazid Danfulani

A wani labari na daban, kyawawan hotuna da bidiyoyin shagalin auren Surayya Sule Lamido da kyakyawan angonta Yazid Danfulani, kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara, sun bayyana.

Hotunan iyalan tsohon gwamnan jihar Jigawan, yan uwa da abokan arziki duk sun halarci wurin daurin auren, fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram.

A shagalin da aka yi na bikin yar gatan ya dauka kala inda aka ganta da angonta, mahaifinta, mahaifiyarta da sauran yan uwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel