Hotuna da Bidiyon kyawawan 'ya'ya matan Yariman Bakura a Shagalin Auren 'Dan uwansu

Hotuna da Bidiyon kyawawan 'ya'ya matan Yariman Bakura a Shagalin Auren 'Dan uwansu

  • Hotunan zuka-zukan 'yan matan gidan Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura, sun matukar birge jama'a
  • Kyawawan 'yan matan hudu reras sun bayyana cikin shiga ta alfarma da kwalliyar zamani a shagalin bikin 'dan uwansu
  • Duk da dalla-dallan 'yan matan sun saka kaya iri daya, biyu daga ciki sun saka mayafai iri daya yayin da sauran biyun suka saka iri daya

Kyawawan hotunan 'ya'ya matan Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura sun matukar birge jama'a a soshiyal midiya.

Kamar yadda fashionseriesng ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga zuka-zukan 'yan matan hudu jere reras gwani sha'awa.

Suna sanye da kaya masu kusan launi daya yayin da suka sha kwalliya irin ta zamani mai matukar birgewa da aji irin na 'ya'yan masu hannu da shuni.

Yariman Bakura
Hotuna da Bidiyon kyawawan 'ya'ya matan Yariman Bakura a Shagalin Auren 'Dan uwansu. Hoto daga fashionseriesng
Asali: Instagram

A bidiyoyin da suka fito, an ga biyu daga cikin 'yan mata sanye da mayafai masu ruwan hoda yayin da biyu daga ciki suka saka mayafai masu launin sararin samaniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babu ko shakka, idan aka ce maka tun daga yanayin 'yan matan da sutturun dake jikinsu, naira ta koka, ba za ayi mamaki ba.

Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima ya angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London

A wani labari na daban, labari da duminsa da Legit.ng ke tattaro muku shine na auren 'dan Sanata Ahmad Sani, Yariman Bakura da za a yi a birnin London.

Kamar yadda @fashionseriesng suka fitar a shafinsu na Instagram, an daura auren a ranar Juma'a, 5 ga watan Augustan 2022 a birnin London.

Ya yi wuff da kyakyawar budurwarsa mai suna Fatima Ali 'yar asalin kasar Somalia a babban Masallacin birnin London.

Asali: Legit.ng

Online view pixel