Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawar Diyar Gwamna Atiku Bagudu

Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawar Diyar Gwamna Atiku Bagudu

  • Ana shagalin bikin Maryam, diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da angonta Ibrahim Gwandu
  • Bidiyoyi da hotunan bikin sun bayyana a shafukan soshiyal midiya inda amarya da ango suka fito shar dasu gwanin sha'awa
  • Matar marigayi tsohon shugaban kasa, Hajiya Maryam Sani Abacha ma ta halarci shagalin kamu da aka yi na bikin

Kebbi - Shagali ya kankama sosai a gidan Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, na auren kyakkyawar diyarsa Maryam Bagudu.

An dai kulla aure ne tsakanin Maryam da hadadden angontamai suna Ibrahim Gwandu.

Duk a cikin shagalin bikin, an gudanar da kasaitaccen bikin Kamu na al’ada wanda ya samu halartan yan uwa da abokan arziki.

Amarya da ango
Bidiyoyi Da Hotunan Shagalin Kamun Auren Kyakkyawa Diyar Gwamna Atiku Bagudu Hoto: Northern_hypelady
Asali: Instagram

Daga cikin wadanda suka halarci bikin Kamun harda matar tsohon shugaban kasa, Hajiya Maryam Sani Abacha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daya daga cikin bidiyoyin bikin da ya yadu a soshiyal midiya, an gano amarya da angon durkushe a gaban Maryam Abacha suna kwasar gaisuwa yayin da ita kuma ta sanya masu albarka.

Hakazalika an gano amarya Maryam da kawayenta suna kwasar rawa yayin da sautin kida ke tashi a dakin taron.

Amarya dai ta sanya kayan alfarma har kala biyu na rigar saki irin wadanda amare ke yayi a yanzu yayin da shi kuma ango Ibrahim ya saka shadda dinkin babbar riga.

Kalli bidiyoyi da hotunan a kasa:

Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

A wani labarin, wani tsoho dan shekaru 90 mai suna Baizirre Jean Marie ya bayyana cewa har yanzu a kasuwa yake baida aure.

Kafar labarai ta Afrimax English ta ziyarci kauyen mutumin kuma sun zanta da shi, inda ya bayyana matsayinsa a soyayya.

Baizire ya bayyanawa kafar labaran cewa ya tsaya ne a aji biyar na makarantar firamare, wanda yace bai tsinana masa komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel