Adamawa: Kotu Ta Umurci A Rataye Shararren Ɗan Damben Gargajiya Har Sai Ya Mutu Saboda Kashe Matarsa Da Duka

Adamawa: Kotu Ta Umurci A Rataye Shararren Ɗan Damben Gargajiya Har Sai Ya Mutu Saboda Kashe Matarsa Da Duka

  • Kotu a Jihar Adamawa ta yanke wa fitaccen dan damben gargajiya Thank-You Grim hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • An yanke wa Thank-You hukuncin ne bayan wadanda suka yi kararsa sun gabatarwa kotu hujojji masu gamsarwa da ke tabbatar da laifin
  • Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar matar, Kwalla, tana son rabuwa da Thank-You ne saboda matsalolin da suke samu ta zo neman saki sai ya kama ta da dambe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Adamawa - Wata kotu da ke Adamawa ta yanke wa wani dan dambe, Thank-You Grim, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe matarsa, Kwalla Grim a karamar hukumar Guyuk.

Babban alkalin jihar Adamawa, Mai sharia Nathan Musa, ya yanke wa dan damben hukuncin kisa bayan kotu ta same shi da laifin kisar kai, rahoton Punch

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

Gudumar Kotu
Adamawa: Kotu Ta Ce A Rataye Dan Dambe Har Sai Ya Dena Numfashi Saboda Kashe Matarsa Da Mugun Duka. Hoto: News Break NG.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Musa, yayin yanke hukuncin a ranar Talata ya ce:

"Masu shigar da karar sun gabatar da gamsassun hujojji da ke nuna wanda aka yanke wa hukuncin ne ya kashe marigayiyar. Don haka aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda sashi na 192(b) dokar Penal Code."

Punch Metro ta rahoto cewa wanda aka yanke wa hukuncin, dan asalin garin Sili a karamar hukumar Guyuk, ya yi sanadin rasuwar matarsa a ranar 24 ga watan Maris na 2018.

A cewar bayanai na kotu, ma'auratan suna fama da matsaloli a aurensu kafin lamarin da ya yi sanadin rasuwar Kwalla a Janairun 2018.

Yadda abin ya faru

Bayan sun rabu, matar ta fara soyayya da wani mutumin kuma ta yanke shawarar za ta aure shi.

Hakan yasa ta matsa wa wanda aka samu da laifin ya sake ta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena', Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

An tattaro cewa Thank-You, wanda da farko ya ki yarda ya sake ta, ya amsa cewa ya yarda, ya kuma gayyace ta gidansa, amma sai ya fara rokonta ta dawo gidansa.

Amma ta ki amincewa.

Wanda aka yanke wa hukuncin, yayin bayyani a kotu ya ce ya fusata bayan Kwala ta fada masa ta masa asiri, Blue Print ta rahoto.

Ya yi ikirarin bai san lokacin da ya kama ta da dambe ya kuma yi amfani da tabarya.

Thank-You ya fatattaki makwabta da suka taho kawo mata dauki bayan sun ji ihun ta.

A cewarsa, shine ya kai kansa ofishin yan sanda na karamar hukumar Guyuk a ranar, inda ya fada wa yan sanda ya halaka matarsa.

Kotu Ta Yanke Wa Basaraken Najeriya Mai Mata 12 Da 'Ya'ya 60 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

A wani rahoto mai kama da wannan, an yanke wa dagacin kauyen Efen Ibom a karamar hukumar Akwa Ibom, Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Bada Umurnin Sake Shari'ar Aminu Yahaya-Shariff, Wanda Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa a Kano

An gurfanar da basaraken ne a kotu kan tuhume-tuhume hudu masu alaka da hadin baki, aka kuma same shi da laifin kashe wani Udoma Udo Ubom, Daily Trust ta rahoto.

A cewar hukuncin da mai shari'ar Edem Akpan na babban kotun Jihar Akwa Ibom ya yanke, an samu basaraken da laifin kisa bayan yi wa mammacin alurar wata guba wadda ta yi sanadin mutuwarsa a ranar 26 ga watan Afrilun 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel