'Saurayina Ya KomaTurai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena': Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

'Saurayina Ya KomaTurai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena': Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

  • Wata matashiyar budurwa ta bayyana yadda ta shiga wani hali a soyayya bayan sauranyinta ya koma Turai da zama
  • Budurwar ta bayyana cewa saurayin nata ya yi kaura ne mako daya bayan ya yi alkawari cewa zai aure ta, lamarin da ya dasa ayar tambaya
  • Mutane da dama sun taya ta murnar cewa mijin nata ya dawo, cewa wasu da suka shiga irin wannan halin basu yi dace ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta je shafin TikTok don bayyana yadda saurayinta ya koma Turai da zama mako daya bayan ya nemi auranta.

A wani bidiyo, budurwar mai suna zaynab_azeez a TikTok ta bayyana cewa mutanen da suka san da naman auren suna ta yi mata ba’a tare da hasashen cewa wata kila soyayyarsu ta bi ruwa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Miji da mata
Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena: Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya Hoto: TikTok/@zaynab_azeez
Asali: UGC

Ta bayyana cewa yan watanni kadan bayan nan, sai mutumin ya dawo Najeriya sannan ya aure ta. Wani bangare na bidiyon ya haskota rike da takardar shaidar aurenta.

Budurwar ta ce komai ya tafi yadda ya kamata kuma kwannan nan za ta je ta same shi a Turai. Matar ta shawarci mutane da kada su bari hasashen mutane marasa kyau ya samu matsuguni a zukatansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tara martani fiye da 400 da ‘likes’ fiye da 23.000.

Kadijat Oritoke ta ce:

“Don ya yi maki aiki ba yana nufin zai yiwa wasu aiki ba…nawa bai yi nasara ba.”

YourGoddessness ta ce:

“Wasu lokutan ba bakin ciki bane. Ta yiwu da gaske sun damu da ke ne, musamman da labaran maza su ki dawowa don cika shirye-shiryen auren.”

Kara karanta wannan

Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba

sunshineglow22 ta ce:

“Ina fatan irin wannan nasarar. Mijina nima yana Birtaniya. Ina addu’a Allah yasa na samu biza.”

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

A wani labarin, wasu masoya bakin fata da Baturiya da suka kulla soyayya ta soshiyal midiya tsawon shekara daya sun hadu ido da ido.

Mutumin mai suna Chris Kizito ya kasance cike da farin ciki yayin da baturiyar budurwar tasa, Jessie ta iso Najeriya.

A wani dan gajeren bidiyo a TikTok, an gano yadda Chris ya rungume ta bayan ya hango ta a filin jirgin sama, yayin da wani dan uwansa ya taimakawa Jessie wajen daukar kayanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel