Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

  • Wani matashi 'dan Najeriya mai suna Michael Polycarp, ya wallafa wani bidiyo inda ya ga mahafinsa a otal tare da wata mata
  • A bidiyon, matashin ya dinga ihun yabawa mahaifinsa kuma ya kira shi da babban yaro ganin yadda ya kamawa mace daki
  • Babu shakka wannan bidiyon ya tada kura a soshiyal midiya inda mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu kan faruwar lamarin

Wani matashi 'dan Najeriya mai suna Michael Polycaro, ya bayyana wani bidiyo mai bada dariya inda ya ci karo da mahaifinsa tare da wata mata a otal.

Matashin da yake cike da mamaki ya dinga nadar bidiyon babansa inda yake yaba masa tare da kiranshi babban yaro.

Papa Lodge
Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata. Hoto daga Michael Polycarp
Asali: UGC

A bidiyon da ya yadu, an ga mahaifin matashin na tafe da wata farar mata zuwa wani otal da ba a bayyana sunansa ba.

Kara karanta wannan

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

A yayin da matar ke ta faman doka murmushi, mahaifin Michael fuskarsa babu yabo balle fallasa kuma ya saka hannuwansa a cikin aljihu, lamarin da ya bar jama'a da tambayoyi kala-kala.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'a sun dinga martani

Daga sakin bidiyon, gayu sun dinga martani kan mahaifin wannan matashi mai budurwar zuciya. ga wasu daga cikin tsokacin jama'a da Legit.ng ta tattaro muku:

@biglion992 yace:

"Mahaifinka da nawa mahaifin duk maza ne 'yan yayi."

@divinefavour579:

"Hannun da ya saka a aljihu ne yafi birge ni."

@queendaline45:

"Saboda kai ne wannan gayen mutumin yace bari ya fito waje ya dan yi shagalinsa, amma duk da haka sai da same shi a wajen."

@anniebo4 :

"Irin wannan mahaifin nake so ai."

@swaveybtc2:

"Kalle shi fa, yana wani gaye har saka hannu yake a aljihu."

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena', Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

@uchey_21:

"Ka siya masa irin kayan ka. Kalla yadda baba yake danye shakaf kamara matashi."

Kalla bidiyon a kasa:

Budurwa ta Kaiwa Saurayi Ziyara, ya Fadi ya Mutu a Bandakin Otal, SP Benjamin Hundeyin

A wani labari na daban, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ja kunne jama'a da su kiyayi kai wa wadanda basu sani ba ziyara ba tare da sun sanar da kowa ba.

Ya bayyana wannan shawarar ne a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi da yammaci.

Kamar yadda Hundeyin ya sanar, wata matashiyar budurwa ta je har Legas domin haduwa da wani mutumi da ta hadu da shi a yanar gizo.

Rashin sa'a da tsautsayin a yi, ya saka ta cikin matsala inda mutumin ya yanke jiki ya fadi ya mutu a bandakin dakin otal din da ya kama musu.

Kara karanta wannan

Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel