Kotu Ta Yanke Wa Basaraken Najeriya Mai Mata 12 Da 'Ya'ya 60 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotu Ta Yanke Wa Basaraken Najeriya Mai Mata 12 Da 'Ya'ya 60 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

  • Babban kotun jihar Akwa Ibom ta yanke wa dagacin kauyen Efen Ibom, Cif Essien Matthew Odiong hukuncin rataya
  • Hukuncin na zuwa ne bayan an samu basaraken da laifin aikata kisar wani Udoma Udo Ubom da yan uwansa suka zarga da maita
  • Cif Odiong ya jagoranci shari'ar maitar ya kuma bukaci mammacin ya yi rantsuwa sannan daga bisani aka masa allurar wata guba da ta yi sanadin mutuwarsa

Jihar Akwa Ibom - An yanke wa dagacin kauyen Efen Ibom a karamar hukumar Akwa Ibom, Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An gurfanar da basaraken ne a kotu kan tuhume-tuhume hudu masu alaka da hadin baki, aka kuma same shi da laifin kashe wani Udoma Udo Ubom, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya Shaidawa ‘Yanuwan Fasinjojin Jirgin da Aka Dauke Ya Bayyana

Gudumar Kotu
Kotu Ta Yanke Wa Basarake A Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar hukuncin da mai shari'ar Edem Akpan na babban kotun Jihar Akwa Ibom ya yanke, an samu basaraken da laifin kisa bayan yi wa mammacin alurar wata guba wadda ta yi sanadin mutuwarsa a ranar 26 ga watan Afrilun 2017.

Dalilin kashe marigayin

Tunda farko, yan uwan marigayin ne suka zarge shi da maita dagan shi kuma dagacin kauyen ya umurci ya yi rantsuwa cewa shi ba maye bane, Punch ta rahoto.

Kotun ta ce bayan basaraken ya gane laifin da ya aikata, "Ya tsere daga kauyen tun a shekarar 2017 bai dawo ba sai 2019, a lokacin kuma yan sanda suka kama shi."

A cewar kotun, gubar da aka yi wa marigayin alurarta ne ta yi sanadin mutuwarsa.

Alkalin ya yanke wa basaraken, mai shekaru 82, hukuncin rataya saboda kisa, daurin shekaru bakwai da aiki mai wahala saboda yin haramtaciyyar shari'a sai kuma daurin shekara uku saboda hadin baki tare da sauran mutanen da ba su riga sun shigo hannu ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Gamu da Cikas Yayin da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Basarake a Kano

Odiong yana da yaya 60 tare da matansa 12.

Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Kashe Sarki a Najeriya Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

A wani rahoton, Babban kotun Jihar Ekiti, ta yanke wa wani mutum, Stephen Ominiyi, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wani da ke jiran gadon sarauta a Ekiti, rahoton Premium Times.

Mr Omoniyi, wanda aka yi ikirarin cewa yana da matsalar tabin hankali, ya daba wa Gbadebo Olowoselu, sarkin Odo Oro Ekiti a wancan lokacin, a karamar hukumar Ikole a Augustan 2018.

Asali: Legit.ng

Online view pixel