Bidiyon Malamin Makaranta Dake Iyo a Rafi Domin Kaiwa Makaranta, Ya Taba Zukatan Jama'a
- Wani shugaban makaranta mai shekaru 36 ya koma yin iyo a rafi kafin ya isa makarantarsa bayan ya rasa mafita
- Mensah Kwame, wanda ya fara koyarwa bayan kammala kwaleji a 2009, ya bayyana yin iyo a rafi zuwa makaranta a matsayin abu mai gajiyarwa
- Matashin malamin ya bayyana cewa rafin da yake shiga na jefa iyalinsa cikin tunani domin a kullun basu da tabbaci kan ko zai dawo gida
Ghana – Wani malamin makaranta mai suna Mensah Kwame, yana iya bakin kokarinsa don ganin yara a wata makarantar firamare ta kakkara mai suna Lonpe MA Primary School da ke yankin arewacin Ghana sun samu ingantanccen ilimi, amma hanyar da yake bi kafin isa makarantar akwai takaici.
Shugaban makarantar mai shekaru 36 ya kan yi iyo a cikin rafi kafin ya isa makarantar kuma ya bayyana hakan a matsayin mai gajiyarwa lokacin da tashar TV3 Ghana ta yi hira da shi.
Malamin ya kan cire tufafinsa a bakin ruwan sannan ya yi iyo a ciki da gajeren wando kafin ya iya ketarawa zuwa daya bangaren don samun kwale-kwale.
Daga nan sai ya shiga kwale-kwalen zuwa inda tufafi da sauran kayansa suke a bakin ruwa kafin su sake tsallakawa zuwa daya bangaren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya fada ma kafar labarai ta kasar Ghana cewa bashi da wani zabi illa kawai ya isa makaranta a wannan yanayi domin ba zai yiwu ba samun masauki a wannan garin.
Iyo da Kwame ke yi a ruwa zuwa makaranta na damun iyalansa
Kwame ya kara da cewa shiga ruwa da yake yi zuwa makaranta yana damun iyalinsa sosai. A cewarsa, a kullun sukan yi tunanin yadda zai dawo gida sanin kalubalen da ke tattare da rafin.
“A matsayin malami a yankin kakkara, dole sai mutum ya tashi da adubahin fari.
“Harma idan za ka tafi, iyalinka su kan kasance cikin zullumi saboda a hanya akwai rafi. Basu da tabbacin kan ko za ka dawo gida bayan makaranta.”
Kwame na amfani da babur wajen shafe tafiyar kilomita tara zuwa makaranta har sai da ta lalace.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama’a a soshiyal midiya
Relax & chill ya ce:
“Wani zai kalli wannan bidiyon sannan ya zo yana kare jam’iyyarsa.”
Larbi Jesila ta ce:
"Aaaaw abun kyama wajen kallo a ido. Allah ya yi maka albarka mallam. Shugabanninmu su ci gaba da tuka manyan motocin alfarma.”
BLAZZING BUZZ ya ce:
“Zai fi a rushe gwamnati sannan mu koma ga tsarin sarauta.
“Muna zabar shugabanni marasa hankali.”
Hotunan Kyakkyawar Budurwar Da Ta Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Arewacin Amurka, Ta Samu Kyaututtuka
A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai suna Fartun wako ta lashe gasar karatun Al-Qur’ani na Imam Shatibi inda ta zo ta daya.
Sakamakon wannan bajinta da kyakkyawar budurwar ta yi an bata kyautar dankareriyar mota kirar 2022 Toyota Highlander sabuwa fil, kudi da kuma kujerar zuwa aikin Umrah.
Kamar yadda shafin Converts to Islam ya wallafa a Facebook, sama da dalibai 530 ne suka shiga gasar a wannan shekarar.
Asali: Legit.ng