Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce

Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce

  • Wata kyakkyawar matar aure ta je shafin yanar gizo don wallafa hotunan mijinta yana taimaka mata wajen yin suya ta hanyar amfani da iccen girki
  • Matar ta yi godiya ga Allah da ya albarkaceta da samun mijin da ke taimaka mata sosai, cewa rayuwa ta yi sauki da mutum irin sa
  • Mutane da dama a Twitter sun yi martani ga wallafar tata cewa samun irin gidanta da wahala a irin wannan zamani da muke ciki

Najeriya - Wata matashiyar mata mai suna Misis Zanga a Twitter ta wallafa wasu hotuna don yabawa mijinta.

Matar a cikin wallafar da ta yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta, ta bayyana cewa mijinta yana taimakonta sosai da sosai.

Mata da miji
Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce Hoto: @MrsZanga
Asali: Twitter

Miji mai taimako

Ta yi godiya ga Allah da ya bata mutumin a matsayin abokin rayuwa. A cikin hotunan, an gano mutumin ba riga yana taimakawa matar a cikin dakin girki.

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin ya tattake yana taimakawa matar tasa yayin da ya mayar da hankali sosai wajen soya abun da ya yi kama da gyada a wani tukunya mai fadi. An gano shi duk ya jike da gumi. Mutane da dama sun yi martani kan wallafar tata a Twitter.

Kalli wallafar tata a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@Missquesto ta ce:

“Kamata yayi ace kyakkyawa kamarki ta auri namiji mai kudi sosai.”

@call_mhi_joker ya yi martani:

“Kin yi gaskiya shiyasa ba za ki taba samun abokin zama ba.”

@MissChurchie ta ce:

“Bayar da kudi da kasancewa mai taimako abu mabanbanta ne guda biyu, yawancin maza za su baka kudi sannan su ja gefe amma wannan? Hakan ya yi kyau sosai.”

@Phoenvvx ta ce:

"Lmfao mazan da ke kokawa a sashin sharhi basu da lafiya sosai. Na tausayawa matanku.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Koyawa Yan Mata Dabaru kan Yadda Za Su Tambayi Iyayensu Maza Kudi

Matashi Dan Shekaru 27 Zai Yi Wuff Da Budurwarsa Mai Shekaru 74 Wacce Ke Tuna Masa Da Kakarsa

A wani labarin, wasu masoya wadanda suka hadu a shafin soshiyal midiya sun bayyanawa duniya irin son da suke yiwa junansu.

Kathi Jenkins mai shekaru 74 ta hadu da Devaughn Aubrey mai shekaru 27 inda suka yi zurfi a soyayya kuma a yanzu haka, masoyan wadanda suka fito daga Texas sun yi baiko kuma za su shiga daga ciki.

Kasancewar sun shafe tsawon shekara fiye da daya a soyayya, Devaugh ya ce ya san tsohuwar mai shekaru 74 ita ce burin ransa, shafin LIB ya rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel