Tsadar Kayayyaki: An Gargaɗi Gwamnatin Buhari Kan Yunwa da Rikicin Sierra Leone

Tsadar Kayayyaki: An Gargaɗi Gwamnatin Buhari Kan Yunwa da Rikicin Sierra Leone

Tashin farasshin kayayyaki da ya kai 19.64 a watan Yuli daga 18.60% a watan Yuni, alama ce da ke nuna tsadar rayuwa na nan tafe a ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Jaridar Punch ta ruwaito hukumar kididdiga ta ƙasa NBS na faɗin cewa tashin farashi zuwa 19.64% shi ne mafi girma da Najeriya ta shaida cikin shekaru 17.

Masana tattalin arziki da sauran masu ruwa da tsaki a fannin, a hira kala daban-daban da jaridar, sun bayyana cewa tashin farashin kayayyaki ka iya haifar da azababbiyar yunwa a kasa, inda a cewarsu Najeriya na fuskantar barazanar zanga-zanga irin wacce ta faru a ƙasar Sierra Leone kwanan nan.

Shugaba Buhari da Ministar kudi.
Tsadar Kayayyaki: An Gargaɗi Gwamnatin Buhari Kan Yunwa da Rikicin Sierra Leone Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake bayani dalla-dalla, shugaban hukumar NBS, Prince Semiu Adeniran, ya ce sun gwada farashin kayayyaki lokaci bayan lokaci da kuma kayan da mutane ke ci a rayuwarsu ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

Adeniran ya ce a watan Yuli, 2022, gwajin shekara-shekara, ya nuna farashin kayayyaki ya kai kashi 19.64%. A jawabinsa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An samu karin kashi 2.27 sama da yadda farashin yake a watan Yuli, 2021, wanda a lokacin yake 17.38%. Hakan ya nuna farashin ya yi sama idan aka kwatanta da na bara, Yuli, 2021."

Farashin kayayyaki a birane ya tashi zuwa kaso 20.09, hakan ya nuna an samu karin 2.08 idan aka yi la'akari da na bara, watan Yuli, 2021 yayin da yake 18.01, inji NBS.

A watan Yuli, 2022, farashin kaya a yankunan karkara ya koma 19.22%, amma a bara watan Yuli, 2022 yana kaso 16.75.

Wane irin rikici ya faru a ƙasar Sierra Leone?

Dambarwa ta balle a ƙasar Sierra Leone a watan Agustan nan da muke ciki biyo bayan tashin gwaurin zabi da farashin kayan abinci ya yi. Gwamnatin ƙasar ta ƙaƙaba dokar zaman gida bayan mutuwar mutum 20, ciki har da yan sanda da fararen hula a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Kamar Najeriya, Farashin kayayyaki sun nunka a ƙasar Sierra Leone cikin watanni 18, inda ya tashi daga 11.9% a watan Fabrairu, 2021 zuwa 24.9% ya jefa talakawa cikin bala'in rayuwa.

Duba da yadda abubuwa ke taɓarɓarewa game da farashin, ƙungiyoyin yan kasuwa sun roki masu gina tsare-tsaren Najeriya da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, su ceto ƙasar nan daga haɗarin da take fuskanta.

Victor Giwa, shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam da fafutar adalci, ya ce Najeriya na kan siraɗin tsunduma cikin rikici kwatankwacin na Sierra Leone domin matsakaitan yan kasar ba zasu iya rayuwa ba.

Saboda haka, ya roki gwamnatin tarayya da ta dawo ta zauna ta yi karatun ta nutsu, da saurari bukatun talakawan ƙasarta.

Darakta Janar na cibiyar ƙasuwancin Amurka, Sola Obadimu, yace rashin tabbas ɗin farashin kayayyaki ya samo asali ne da jagorancin tattalin arziƙi mara kyau kuma haka zai kai kasar ya baro.

A cewarsa,

Kara karanta wannan

Kaico: Dan takarar shugaban kasa ya soki su Buhari saboda gaza gyara wutar lantarki

"Akwai illolin rashin tafiyar da tattalin arziki yadda ya dace, shiyasa kuka ga mutane na ta kwarara suna fice wa daga ƙasar, illa ce ta tattalin arzikin da ya gaza."
"Kudin ƙasa na zama mara amfani ba su da daraja, ba'a tafiyar da arziki yadda ya kamata, bai kamata ace gwamnan CBN ke da wuka da nama a tafiyar da tattalin arziki ba, akwai nauye-nauyen da ke kansa. Farashin kaya ba shi da tabbas."
"Yau zaka siya abu N2 gobe zaka same shi N5, idan ka koma mako na gaba zaka sake taras da ya tashi. Ba wanda ke wani abu game da haka, yanzu muna zancen Mayu, 2023, waya san me zai faru daga yanzu zuwa lokacin?"

Ya shawarci gwamnati ta koma asalin tushen tafiyar da tattalin arzikin ƙasa domin guje wa rushe wa baki ɗaya, wanda a hasashensa zai bar babban kalubale ga gwamnati mai zuwa.

Lucky Amiwero, shugaban majalisar daraktocin kwastam, ya yi kira ga gwamnati ta canza fasalin tattalin arziki domin guje wa haɗarin da ke tafe.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Ya ce akwai kashe-kashen kuɗaɗe da gwamnati ke yi waɗan sam ba su da amfani, "Akwai bukatar canza fasalin tsarin, gwamnati ta cika kashe kuɗi kuma da yawan su mara amfani."

"Jirage masu zaman kansu nawa gare mu a Najeriya? Zaku ga mafi yawan gwamnoni tare da jami'an tsaro ta ko ina, shin su tashin farashin bai shafe su bane? Idan ka diba abun zaka yi hasashe."
"Idan ka kalli yadda ake sace Mai da sauransu, zaka fahimci ba abinda ke tafiya dai-dai. Gwamnati na kashe kuɗi mara amfani, cin hanci ya yi yawa, komai ya juya sama zuwa ƙasa."

Najeriya bata samar da komai

Da yake tsokaci, Shugaban ƙungiyar masu safarar kayayyaki masu rijista a Najeriya, Frank Ukor ya ce:

"Ka duba farashin da ake musayar kuɗi, ban san me zamu iya yi ba saboda ba wani abu da muke samar wa. Da ace muna kirkirar wani abu ne, zan iya cewa zamu iya wani abu don ɗaga darajar Naira."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

"Zaɓin da ya rage mana shi ne zaɓe na zuwa shekara ta gaba, dole mu tashi mu zaɓi wanda ya dace, mu canza kasar mu daga mai bukata zuwa mai samar da abubuwa. Muna bukatar fara sarrafa abubuwa, mun can gurbatattun shugabanni."

A wani labarin kuma El-Rufai da Shugabannin Arewa Ta Yamma Sun Gabatar Wa Tinubu Jerin Manyan Muƙaman da Suke Bukata

Shugabannin APC reshen arewa maso yammacin ƙasar nan sun rubuta tare da gabatarwa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa, jerin mukaman da suke buƙata idan an kafa gwamnati a 2023

Wasu bayanai da suka fito sun nuna cewa gabanin Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa, gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, ya jagoranci tawagar wakilan arewa ta yamma zuwa wurinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262