'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

  • Shugaban TESCON ya shiga matsala kan tsokacin da aka kwatanta shi da na rashin ladabi da yayi kan ministan yankin arewa, Alhaji Saani Alhassan
  • Sayibu Afa Yaba, shi ne Shugaban TESCON a jami'ar fasaha ta Tamale, ya wallafa cewa kamar ministan bai yi wanka ba kafin ganawa da Shugaban kasa
  • An zargi cewa, 'yan sanda sun je har makaranta sun yi ram da shi a ranar Laraba, 10 ga watan Augustan 2022 zuwa wani wuri da ba a sani ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ghana - Shugaban kungiyar dalibai na jami'ar fasaha ta Tamale dake Ghana, Sayibu Afa Yaba, ya shiga hannun jami'an ,yan sanda.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama shi a ranar 10 ga watan Augustan 2022 kan wani tsokaci da yayi a soshiyal midiya da ake gani tamkar cin mutuncin ministan yankin arewaci, Alhaji Saani Alhassan.

Kara karanta wannan

Faifan Bidiyo Mai Ban Tsoro Ya Nuna Yadda wani Dan Saudiya Ya Fadi Ya mutu Yana Kan Jawabi

Ghanian Minister
'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa. Hoto daga Ghanaweb
Asali: UGC

Sayibu ya wallafa a Facebook cewa, alamu na nuna cewa Alhaji Alhassan bai yi wanka ba lokacin da ya jagoranci tawagar yi wa shugaba Akufo-Addo maraba a babban birnin yayin da yaje rangadi.

Kamar yadda rahotanni suka nuna daga Ghanaweb, kungiyar dalibai din ta sha mamaki kan wannan kamen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna cikin makaranta yayin da wani jami'in 'dan sanda ya jagoranci tawaga suka kama abokin karatunmu. Daga yanda ya gabatar da kansa, zatonmu wasa ne. Kawai sai muka ga ya buga masa ankwa a hannu tare da aike shi caji ofis," shugaban SRC, Dauda Gafaru ya sanarwa gidan rediyon Tamale.
Ya kara da cewa: "Har tambayarmu aka yi idan ya dace yadda abokin karatunmu yayi wa ministan a Facebook," yace hakan ya tabbatar da cewa kamen an yi shi ne saboda wallafarsa ta Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Bidiyo: 'Dan Sandan Najeriya Ya Fitittike, Ya Ki Karbar Kudin da Direba Ya Bashi Kyauta

A wani labari na daban, wani jami'in 'dan sanda ya bayyana wadatar zucinsa a kan titi da irin albashin da yake samu ya ishe shi, lamarin da ya matukar birge jama'a.

Lamarin ya faru ne inda 'dan sandan ya ki karbar kudin da mutumin dake cikin mota ya bashi. 'Dan sandan ya jaddada cewa bai zai karba kyautar ba.

Bayan mutumin ya ga ya dinga mika kyautar kudinsa kuma an ki karba, ya fito da wayarsa inda ya nadi bidiyon jami'in 'dan sandan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel