Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

  • Goodluck Jonathan ya halarci taron da aka yi domin tunawa da Marigayi Kyaftin Hosa Okunbo
  • Tsohon Shugaban kasar ya yi kira ga mutane da su guji zaben ‘yan siyasa saboda samun na cefane
  • Adams Oshimhole da Dino Melaye sun halarci taron, sun kuma jinjinawa Dr. Jonathan

Abuja - Goodluck Jonathan yace shugabannin farko da aka yi sun gagara hada-kan al’umma saboda sun sa bangaranci a gaba, a maimakon kishin kasa.

Punch ta kawo rahoto a ranar Asabar, 13 ga watan Agusta 2022 cewa Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana haka da ya gabatar da wata lacca a garin Abuja.

An shirya taro domin tunawa da Kyaftin Hosa Okunbo bayan cika shekara da ya da rasuwarsa, Dr. Jonathan ya gabatar da takardarsa a kan cigaban kasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

A cewar tsohon shugaban Najeriyan, shugabannin farkon da aka yi sun gaji kasar ne bayan an kacancanata zuwa bangarori uku, daga baya ta zama hudu.

Jonathan yace tubalin hadin-kai a lokacin da aka samu ‘yancin kai ba su da karfi, kuma shugabannin kasar ba su yi kokarin karfafa dankon zumunci ba.

An canza tsarin a lokacin da Najeriya ta bar salon yankuna, aka fara amfani da tsarin tarayya, hakan ne ya sa kallon da al’umma suke yi wa kasar ta canza.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan a taro Hoto: @jonathangoodluck
Asali: Facebook

Siyasar kudi a Najeriya

An rahoto Jonathan wanda ya yi mulki tsakanin Mayun 2010 da Mayun 2015 yana mai bada shawara ga mutane su yi zabe, amma su kauracewa siyasar kudi.

“Dole mu gujewa siyasar da ake samun na cefane”

Ezekwesili sun halarci zaman

Tsohuwar Ministar ilmi, Madam Obiageli Ezekwesili ta halarci taron, tayi kira da babbar murya ga ‘yan siyasa su maida hankali wajen bunkasa harkar ilmi.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Obiageli Ezekwesili take cewa muddin ba a farfado da harkar ilmi ba, ba za a samu cigaba ba.

Haka zalika Adams Oshiomhole da Dino Melaye sun halarci taron, suka yabawa tsohon shugaban kasar kan nasarorin da ya samu a lokacin da yake ofis.

Oshiomhole yace Jonathan ya bar tarihi a dalilin kafa makarantun Almajirai da ya yi, yace bai kamata a samu yara su na yawo a titi, ba tare da makaranta ba.

Ana zargin Trump da laifi?

A ranar Juma'a aka ji labari ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka tana binciken tsohon shugaba, Donald Trump da zargin sabawa dokar sirri na kasar Amurka.

Jami’an FBI sun dura gidan tsohon shugaban kasar, sun bincike dakuna domin samun bayanai. Trump ya musanya zargin da ake yi masa a shafinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel