2023: Peter Obi Ya Caccaki APC da PDP Kan Gaza Gyara Wutar Lantarki Tsawon Shekaru 24

2023: Peter Obi Ya Caccaki APC da PDP Kan Gaza Gyara Wutar Lantarki Tsawon Shekaru 24

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya sake yi wa jam’iyyar APC da PDP ruwan kalamai masu zagi kan mulkin ganganci a Najeriya
  • Obi ya koka da yadda jam'iyyun biyu suka gaza samar da wadatacciyar wutar lantarki a tsawon mulkinsu na shekaru 24
  • Peter Obi na yawan sukar gwamnatocin da suka gabata, inda yake wanke kansa duk da kasancewar daya daga cikinsu a baya

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki da PDP kan gazawar da suka yi a bangaren mulki tsawon shekaru.

Kamar yadda jaridar Daily Independent ta ruwaito, Obi ya yi tsokaci kan gazawar jam’iyyun siyasar biyu ne wajen gyara wutar lantarki bayan shafe shekaru 24 a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

An ruwaito Mista Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin kai tsaye.

Yadda dan takarar LP Peter Obi ya caccaki APC da PDP
2023: Peter Obi Ya Caccaki APC da PDP Kan Gazawar Gyara Wutar Lantarki Tsawon Shekaru 24 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta tattaro, Obi ya bayyana yadda jam’iyyun PDP da APC suka yi abin kunya, inda ya ce har yanzu wutar lantarkin Najeriya ba ta tashi daga 4,000 zuwa 5,000 a cikin shekaru 24 da suka gabata ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“Abu mai sauki da ‘yan Najeriya za su tambayi kansu shine, mun shafe shekaru 24 muna abu daya, shin muna kan hanya madaidaiciya? Idan kun kasance a cikin yanayi na shekaru 24, mutane suna ta alkawari amma ba sa cikawa.
“Ku dubi jam’iyyun biyu, sun cika abin da suka yi alkawari? A cikin shekaru 24, Najeriya ba ta iya samun kari a samar da wutar lantarki daga 4,000 zuwa 5,000 ko 6,000 ba.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

"Ka tambayi kanka wannan tambayar, shin za mu ci gaba da wannan? To, za ku ci gaba da bin hanya marar kyau ne ko kuma za ku juya ku ce 'ku saurara, dole ne mu yi abin da ya dace'?"

Kafin wannan batu na Peter Obi, a baya jaridar This Day ta ruwaito shi yana cewa, gwamnatin PDP da APC sun ci bashin $500bn a cikin shekaru 20 na mulkinsu.

Ni na cancanci shugabancin Najeriya, inji Obi

A gafe guda, Obi ya nanata matsayinsa na cewa yana da abin da zai kai ga sake dawo da Najeriya cikin taitayinta.

Ya bayyana haka ne tare da tuna a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, inda ya bayyana cewa magabatansa na magana karara a gare shi a matsayin wanda ya fi cancanta ya gaje kujerar Buhari.

A cewarsa:

“Akwai abubuwa da yawa da zaku iya warwarewa ta hanyar tattaunawa da magana. Zan zagaya kowace jiha ta Najeriya. A Anambra nakan yi rangadi a kowace karamar hukuma sau daya a kowane wata uku kuma ina kwana a kowace karamar hukuma."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

Ya bayyana cewa, zai gwada wannan dabi'a ta ziyara da kokarin hada kan 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Tashin Hankali a APC Yayin da Jam’iyyar Ta Gaza Mayarwa ’Yan Takarar da Suka Janye Kudin Fom

A wani labarin na daban, watanni hudu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a mayar wa ‘yan takarar da suka janye daga takarar APC a taron gangami na ranar 26 ga Maris, har yanzu jam’iyyar ba ta bi umarninsa ba.

Bincike ya kuma nuna cewa ‘yan majalisar da suka gudanar da taron na kasa (daga unguwanni zuwa matakin kasa) na bin APC kudade gabanin babban zaben 2023.

Jam’iyyar, a cikin watanni biyun da suka gabata, ta kuma gaza wajen biyan albashin ma’aikata kamar yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel