Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada attijirin Afirka, Aliko Dangote shugaban kwamitin kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro (Maleriya) a Najeriya
  • Sauran mambobin kwamitin sun hada da Tony Elumelu, shugaban UBA, Femi Otedola, Shugaban Forte Oil, Folurunsho Alakija, Shugaban, Rose of Sharon Group da saraunsu
  • Aliko Dangote ya a jawabinsa ya mika godiya na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yi alkawarin zai yi iya kokarinsa don ganin an cimma burin kafa kwamitin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata kafa kwamiti mai mutum 16 na kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro (maleriya) a Najeriya, tare da nada Aliko Dangote a matsayin shugabanta.

Ya ce aiwatar da aiwatar da shirin kwamitin cikin nasara tare da kawar da cutar zai sa Najeriya ta adana kimanin Naira biliyan 687 a 2022 da Naira tiriliyan 2 zuwa shekarar 2030.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Dangote da Buhari.
Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Buhari ya ce baya ga inganta lafiyar yan Najeriya da walwalarsu, shirin na kawo karshen maleriya na da tasiri ga lafiyar al'umma da tattalin arzikin kasa, kakakin Buhari, Bashir Ahmad ya sanar a shafinsa na Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Cutar Maleriya na iya janyo mummunan ciwo da matsaloli ga mata masu ciki kuma yana sanadin karuwar bari na juna biyu.
"Yana kuma sanadin mutuwar jarirai da kananan yara, inda ya fi shafan wadanda ba su kai shekaru biyar ba.
"Wadannan sune dalilan da yasa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wurin yaki da maleriya," in ji Buhari.

Buhari ya yi bayanin cewa an nada Dangote mukamin ne saboda ayyukan da ya yi a baya da shaukinsa na tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Dattawa Sun yi Magana a kan Yunkurin Radawa Kaduna Sabon Suna

Martanin Dangote

A jawabinsa, Dangote ya gode wa shugaban kasar da sauran mambobin kwamitin saboda danka masa wannan babbar nauyin, ya yi alkawarin zai yi aiki tukuru don ganin ya cimma nasara.

Ya ce sabon nadin da aka masa ya dace da matsayinsa na Jakadar Najeriya na yaki da Maleriya.

Mambobin kwamitin na kawo karshen Maleriya a Najeriya

Mambobin kwamitin sune: Ibrahim Shehu, Sakataren dindindin, ofishin mataimakin shugaban kasa kan harkokin siyasa da tattalin arziki, da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Saura sun hada da Yahaya Oloriegbe, shugaban kwamitin lafiya na majsalisar dattawa, Hon Abubakar Dahiru, Ciyaman, Kwamitin majalisar wakilai kan Kamjamau, TB da Maleriya, Dr Ehanire, Hon, Ekumankama, Mahmuda Mamman, Sakataren dindindin, Ma'aikatar Lafiya.

Sai kuma Tony Elumelu, Ciyaman, Kwamitin Direktoci, UBA, Folurunsho Alakija, Shugaban, Rose of Sharon Group, Herbert Wigwe, Shugaban, Access Bank, Femi Otedola, Shugaban Forte Oil da Lami Lau, Shugaba, Kwamitin Kasa na Kungiyoyin Mata.

Kara karanta wannan

Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi

Saura sune, John Cardinal Onaiyekan, Archbishop na Katolika a Abuja, Rafiyat Sanni, Amira ta Kasa, Federation of Muslim Women Nigeria, FOMWAN, da Dr Perpetua Uhomoibhi, Shugaban Kungiyar Kawar Da Cutar Maleriya a Najeriya, NMEP.

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

A wani rahoton, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan kasuwa da su rika amfani da dabaru don habaka fannonin tattalin arziki, tare da yin tasiri mai tsawo wajen samar da ayyukan yi da rage radadin talauci.

Ya ba da wannan sahwara ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban rukunin masana'antun Dangote, Aliko Dangote da mambobin rukunin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel