Yadda Gwamna El-Rufai da Jiga-Jigan APC a Arewa Ta Yamma Suka Bukaci Muƙamai a Gwamnatin Tinubu

Yadda Gwamna El-Rufai da Jiga-Jigan APC a Arewa Ta Yamma Suka Bukaci Muƙamai a Gwamnatin Tinubu

Shugabannin APC reshen arewa maso yammacin ƙasar nan sun rubuta tare da gabatarwa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa, jerin mukaman da suke buƙata idan an kafa gwamnati a 2023

Wasu bayanai da suka fito sun nuna cewa gabanin Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa, gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai, ya jagoranci tawagar wakilan arewa ta yamma zuwa wurinsa.

Jaridar Vanguard ta ce El-Rufai ya gabatar wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC wata takarda da ke ƙunshe da bukatun a baiwa arewa ta yamma kujerun mataimaki, Sakataren gwamnati, ma'aikatun kuɗi, ayyuka, Noma, Abuja da harkokin cikin gida.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Yadda Gwamna El-Rufai da Jiga-Jigan APC a Arewa Ta Yamma Suka Bukaci Muƙamai a Gwamnatin Tinubu Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

A bayanan da takardar da ƙunsa, shugabannin APC na arewa maso yamma sun nemi ɗan takarar da uwar jam'iyya ta ƙasa su ware wa yankin muƙamai da suka haɗa da, ofishin mai ba da shawara kan tsaro, hukumar NIMASA.

Sauran su ne, hukumar sufurin ruwa NPA, Bankin NIRSAL, bankin Noma, Bankina BOI, hukumar tsaron farin kaya DSS da hukumar ƙanana da matsakaitan masana'antu SMEDAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin shiyyar arewa ta yamma, yayin gabatarwan, sun ce duba da muhimmancin yankin da gudummuwar da zai bayar wajen lashe zaɓe mai zuwa, ya kamata baki ɗaya muƙaman da suka lissafo a ware wa yankin.

Amma jagoran APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya tafi kai tsaye ya gaggauta ayyana ɗan takarar mataimaki da ya zaɓo, ya kuma ɗauki sauran bukatun su.

Arewa maso yamma da bukatunta

A halin yanzun shiyyar arewa maso yamma tana da ma'aikatun tarayya Tara, waɗan ke wakiltar jihohin Jigawa, Kano, Kaduna, Kebbi, Katsina, Sakkwato da Zamfara.

Shugabannin yankin sun roki cewa wajibi gwamanti mai zuwa ta shawo kan matsalar tsaron da ta zama ƙarfen kafa a yankin, musamman ta'addancin yan bindiga da garkuwa.

Sun kuma buƙaci imganta ilimin yankin, musamman yaran ɗa ke yawo kan titi basu zuwa makaranta, haka nan gwamnatin ta maida hankali kan inganta noma a yankin da raya masana'antu da sauran su.

Shugabannin APC na yankin sun kafa hujjar tattaro waɗan nan bukatun da rawar da gwamnonin yankin suka taka don tabbatar da dai-daito da adalci wajen mulkin karba-karba lokacin zaɓen fidda gwani.

A cewar takardar wacce ta tattaro tarihin yadda yankin ya ba da gudummuwar lashe kujera lamba ɗaya, jagororin sun ƙara da cewa arewa maso yamma ke da makullin canza wasan a 2023.

"Arewa maso yammaci ta taka rawa wajen nasarar APC a zaɓem 2015 da 2019 ta hanyar lashe jihohi Bakwai cikin Bakwai Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa."

A wani labarin kuma Sanatoci na shirin tsige shi, wata jam'iyyar Adawa ta goyi bayan kira ga Shugaba Buhari ya yi murabus

Jam'iyyar ADC ta goyi bayan kiran da ɗan takararta na shugaban ƙasa ya yi ga shugaba Buhari ya yi murabus.

Dumebi Kachikwu, ya nemi Buhari ya sauka daga kujerar shugaban ƙasa tun da ba zai iya kare rayukan yan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel