'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Nasarawa, Sun Kashe Malami

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Nasarawa, Sun Kashe Malami

  • Yan bindiga sun kai sabon hari GSS Nassarawa-Eggon, a jihar Nasarawa, sun harbe wani malami ɗaya har lahira
  • Wani malami da ya memi a ɓoye bayanansa ya ce maharan sun kutsa makarantar da daren Asabar kuma suka nufi gidan mamacin kai tsaye
  • Hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce dakarunta sun bazama da nufin cafko maharan

Nasarawa - Wasu miyagun yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai kazamin hari makarantar Sanadiren kimiyya da ke Nassarawa-Eggon, jihar Nasarawa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Maharan sun bindige malamin makarantar har lahira, wanda aka gano sunansa, Auta Nasela.

Wani Malamin makarantar wanda ya nemi a sakaya bayanansa ya faɗa wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa, NAN, cewa harin ya auku ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Sake Naɗa Tsohon Hadiminsa da Ya Yi Murabus, Ya Ba Shi Babban Matsayi

Sabon hari a Nasarawa.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Nasarawa, Sun Kashe Malami Hoto: premiumtimesng
Asali: Twitter

Ya ce yan bindiga sun kutsa kai ta tsiya cikin makarantar kuma suka tafi kai tssye gidan mamacin, suka bukaci ya fito musu da kuɗi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamain ya kara da cewa wanda aka kashe ya samu nasarar tserewa zuwa gidan maƙocinsa, amma ɗaya daga cikin yan bindigan ya binciko shi kuma ya harbe shi.

A cewarsa, maharan sun kuma harbi wani Malamin na daban kuma, Timothy Malle, amma ya tsira, yanzu haka yana kwance a Asibiti.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Punch ta rahoto cewa da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar yan sandan Nasarawa, Ramhan Nansel, ya ce Kes ɗin na da alaƙa da fashi da makami.

Ya ce:

"Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 8:55 na daren jiya cewa wasu yan bindiga sun shiga GSS Nassarawa-Eggon, sun kutsa gidan Auta Nasela. Da suka shiga sun nemi kuɗi amma mutumin ya tsere gidan makocinsa.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Masu Safarar Kwayoyi da Yan Bindiga Sama da 100 a Jihar Arewa

"Ɗaya daga cikin maharan ya bi sawunsa ya bindige shi. Yan sanda sun yi gaggawar garzaya wa da shi Asibiti amma Allah ya karɓi rayuwarsa ana cikin ba shi kulawa."

Kakakin yan sandan ya ce tuni jami'ai suka kaddamar da bincike kan lamarin da nufin zakulo maharan su girbi aikin da suka shuka.

A wani labarin kuma Sojojin sama da ƙasa sun hallaka dandazon yan ta'adda a Kaduna, sun kwato makamai

Sojojin Sama da Ƙasa sun yi luguden wuta kan sansanin yan ta'adda a yankin karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya ce sojojin sun hallaka yan ta'adda da dama, sun kwato makamai da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel