Sojojin Sama da Ƙasa Sun Hallaka Dandazon Yan Ta'adda a Kaduna, Sun Kwato Makamai

Sojojin Sama da Ƙasa Sun Hallaka Dandazon Yan Ta'adda a Kaduna, Sun Kwato Makamai

  • Sojojin Sama da Ƙasa sun yi luguden wuta kan sansanin yan ta'adda a yankin karamar hukumar Chikun jihar Kaduna
  • Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya ce sojojin sun hallaka yan ta'adda da dama, sun kwato makamai da sauran su
  • Wannan nasarar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Jirgin Sojin NAF ya halaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Alhaji Shanono

Kaduna - Dakarun Sojin Operation Natsuwa sun halaka dandazon yan ta'adda a wani samamen shara da suka kai yankin ƙaramar hukumar Chikun, a jihar Kaduna

Channels tv ta ce wannan nasara na ƙunshe ne a rahoton ayyuka da hukumomin tsaro suka aike wa gwamnatin jihar Kaduna.

Kayan aikin da aka kwato.
Sojojin Sama da Ƙasa Sun Hallaka Dandazon Yan Ta'adda a Kaduna, Sun Kwato Makamai Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar, ya ce yan ta'addan sun baƙunci lahira ne a hannun Sojojin ƙasa da tallafin sojin sama a wani samame da suka kai Gulbi, yankin Chikun.

Kara karanta wannan

An Bankado Wasikar Da El-Rufai Ya Rubutawa Buhari, Yana Sanar Da Shi Shirin Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Kaduna

A cewar Aruwan, "Sojojin rundunar Operation tsaftace daji da taimakon dakarun hukumar sojin sama sun kaddamar da wani samamen kakkaɓe wa kan mafakar yan ta'adda da aka gano a yankin Galbi."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan ya bayyana cewa Sojojin sun kutsa kai har suka keta tafkin Kaduna, duk da yan ta'addan sun yi kokarin maida martani amma Sojin sun nuna jajirce wa suka kashe su da dama a musayar wuta.

Ya ce Sojin sun kwato babbar bindiga mai carbi guda biyu, AK-47 guda uku da Babura Bakwai daga maɓoyar yan bindigan bayan sun tura su lahira.

Gwamnatin Kaduna ta yi martani

Gwamnatin Kaduna ta nuna jin daɗinta da wannan labarin, kuma ta yaba wa gwarazan sojojin bisa jajirce wa da cimma wannan gagarumar nasara akan maƙiya zaman lafiya.

Ta kuma gode wa Sojojin ƙasa da na sama, yan Sanda da yan banga waɗan da suka ba da gudummuwa har aka samu nasara a wannan samamen.

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

Bugu da ƙari, gwamnatin ta roki baki ɗaya hukumomin tsaro su ƙara matsa kaimi wajen kawar da yan ta'adda daga doron ƙasa domin mutane su samu walwala da zaman lafiya, Vanguard ta rahoto.

A wani labarin kuma Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Hallaka Kasurgumin Ɗan Bindiga, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Hukumar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce Jirginta ya halaka kasurgumin ɗan ta'adda, Alhaji Shanono, da wasu mayaka a Kaduna.

Jirgin ya kuma yi raga-raga da maboyar su da kayan aiki a kauyen Ukambo mai kilomita sama da 100 tsakaninsa da garin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel