Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo

Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo

  • Islam, diyar tsohon zababben gwamnan jihar Zamfara, Mukhthar Idris Koguna, ta amarce da kyakkyawan angonta
  • Domin nuna farin ciki a wannan rana, mahaifinta ya yi mata kyautar dankareriyar sarka da ya gada a wajen mahaifiyarsa
  • Tuni bidiyon shagalin ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma ya kayatar da mutane da dama

Zamfara - Kyakkyawar diyar tsohon zababben gwamnan jihar Zamfara, Mukhthar Idris Koguna mai suna Islam ta shiga daga ciki.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano zukekiyar amaryar cikin wata hadaddiyar doguwar riga irin na amaren zamani, kanta lullube da mayafi wanda aka jerawa duwatsu.

Abun birgewa kuma shine mahaifin nata da kansa ne ya daura mata wani dankararren sarkan wuya mai kyau domin cika adonta.

Kara karanta wannan

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

Amarya da mahaifinta
Diyar Tsohon Zababben Gwamnan Zamfara Ta Shiga Daga Ciki, Ya Yi Mata Kyautar Dankareriyar Sarka A Bidiyo Hoto: theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

Kamar yadda yake rubuce a jikin bidiyon wanda shafin theweddingstreet_ng ya wallafa a Instagram, an tattaro cewa mahaifin nata ya yi mata kyautar sarkan ne wanda shima ya gada ne a wajen mahaifiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya zo a rubuce cewa ita kanta mahaifiyar tasa, mijinta wato mahaifinsa ne ya yi mata kyautar sarkan wasu shekarun baya a kasar Saudiyya.

Bayan y agama sanya mata sarkan, sai aka gano amaryar ta rungume mahaifin nata don nuna jin dadi da godiyarta a gare shi, daga nan sai ya jero tare da diyar tasa domin yi mata rakiya zuwa waje.

Jama'a sun yi martani

latest_fabrics_and_more_ ta ce:

"masha Allah."

mammam_suphanor

"Abun ya yi kyau matuka."

Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

A wani labarin kuma, mun ji cewa a ranar Juma’a, 5 ga watan Agusta ne aka daura auren Muhammad Bello, 'dan Sanata Ahmad Sani Yarima a kasar Landan.

Kara karanta wannan

Kansar Bogi: Yadda 'Yan Damfara ke Amfani da Yarinya Mai Shekaru 9 Wurin Tatsar Miliyoyi Daga Jama'a

An dai daura auren Bello ne da kyakyawar budurwarsa mai suna Fatima Ali 'yar asalin kasar Somalia a babban Masallacin birnin Landan.

Sai dai kuma, an dawo gida Najeriya inda ake ci gaba da shagalin biki irin na al’adar mutanen arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel