Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyon wata amarya da ya yadu a shafukan soshiyal midiya
  • Wasu karatan mata ne suka ciccibo amaryar wacce ta sha ado tare da kishingida a kan wani gado tamkar na sarauta
  • A cikin bidiyon da ya yadu, an gano amaryar tana ta murmushi yayin da wadanda suka daukota ke gwagwarmaya da gadon da aka daurota a kai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Idan ana maganar iya shirya biki na gargajiya wanda ke nuna tsantsar al’ada toh ba za a taba barin mutanen yankin arewacin kasar nan a baya ba.

Kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka gudanar da bikin wata kyakkyawar amarya cikin salo.

A bidiyon wanda shafin hausaroom ya wallafa a Instagram, an gano amaryar kishingide a kan wani gado irin na sarauta ta sha ado irin na amare yayin da fuskarta ke dauke da murmushi mai sace zuciya.

Amarya
Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta Hoto: hausaroom
Asali: Instagram

Bayan ta dan kishingida a kan dan tasar da aka ajiye a saman gado, sai ga wasu karatan mata sun ciccibo gadon kacokan da ita a kai zuwa filin liyafar wanda ke dauke da dumbin mutane masu jiran shigowar amarya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan abu ya baiwa mutane da dama mamaki inda mabiya shafukan na soshiyal midiya suka tofa albarkacin bakunansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

helwayat_by_helwa ta yi martani:

“Bilkisu mai gadon zinari.”

swiss_lacess ta ce:

“Ikon Allah! Sai zabga daroya take abinta.”

spices_dot_com ta rubuta:

“ahap ni nasan wnn abun sai y zama yayi.”

eeshaladykidscorner ta ce:

“Ikon Allah!”

sumeebelels_cuisine ta ce:

“Matan ma se kokawa wannan ai aikin maza ko siblings dinta maza in tana da ko a cikin family haka, masha Allah, Allah ya basu zaman lafya.”

Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa

A wani labarin kuma, Black Nells ya karfafawa mazajen da suka yanke kauna da samun soyayya ta gaskiya saboda talauci da ya masu katutu gwiwa a TikTok.

Yayin da yawanci matan yanzu ke neman ‘manyan Alazawa da suka ci suka tada wuya’, Nells ya bayar da labarin sauyin da ya samu don tabbatar da cewar har yanzu ana iya samun mata da ke tsayawa tsayin daka da mutum har zuwa lokacin da zai yi nasara a rayuwa.

Nells ya hadu da masoyiyarsa wasu yan shekaru da suka gabata lokacin da gari ya yi masa zafi. A cewarsa, ya kasance talaka kuma mummuna a wancan lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel