Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle

  • Bidiyo sun bayyana dfaga shagalin bikin Muhammad Bello, 'dan Sanata Ahmad Sani Yarima da zukekiyar amaryarsa
  • An dai daura auren nasu ne aranar Juma’a, 5 ga watan Agusta a Birnin Landan inda aka dawo Najeriya yin shagali
  • A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an gano kyakkyawar amaryar sanye da kayan saki, inda aka kuma sanyawa ango lalle

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - A ranar Juma’a, 5 ga watan Agusta ne aka daura auren Muhammad Bello, 'dan Sanata Ahmad Sani Yarima a kasar Landan.

An dai daura auren Bello ne da kyakyawar budurwarsa mai suna Fatima Ali 'yar asalin kasar Somalia a babban Masallacin birnin Landan.

Sai dai kuma, an dawo gida Najeriya inda ake ci gaba da shagalin biki irin na al’adar mutanen arewa.

Kara karanta wannan

Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa

Amarya da ango
Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle Hoto: theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amarya Fatima cikin adon irin na amaren Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amaryar ta fito shar da ita cikin ado na kayan saki da lullubi inda ta gaji da haduwa don tsananin kyawu da ta yi.

Hakazalika, an gano ango Bello zaune a wajen liyafar bikin yayin da wasu taron mata suka zagaye shi suna sanya masa lalle.

Kalli bidiyon a kasa:

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

A gefe guda, idan ana maganar iya shirya biki na gargajiya wanda ke nuna tsantsar al’ada toh ba za a taba barin mutanen yankin arewacin kasar nan a baya ba.

Kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka gudanar da bikin wata kyakkyawar amarya cikin salo.

Kara karanta wannan

Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije

A bidiyon wanda shafin hausaroom ya wallafa a Instagram, an gano amaryar kishingide a kan wani gado irin na sarauta ta sha ado irin na amare yayin da fuskarta ke dauke da murmushi mai sace zuciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel