Kansar Bogi: Yadda 'Yan Damfara ke Amfani da Yarinya Mai Shekaru 9 Wurin Tatsar Miliyoyi Daga Jama'a

Kansar Bogi: Yadda 'Yan Damfara ke Amfani da Yarinya Mai Shekaru 9 Wurin Tatsar Miliyoyi Daga Jama'a

  • 'Yan damfara da suke yin amfani da wata yarinya mai shekaru 9 mai cutar kansar bogi sun samu miliyoyi daga jama'a
  • Bidiyon mai matukar taba zuciya yana kunshe da yarinya mai suna Alexandria, ya dinga yaduwa inda yake nuna karamar yarinya cikin tashin hankali
  • Sai dai bincike sun bayyana cewa, dukkan abun damfara ce da yaudara wacce aka shirya don samun kudin tallafi daga jama'ar da basu san komai a kai ba

Alexandria, wata yarinya karama mai shekaru 9 da ake yadawa tana fama da cutar kansa a bidiyoyin da suka karade kafafen sada zumuntar zamani ta bai wa jama'a tausayi.

"Ku taimaka min, bana son mutuwa," Alexander take cewa a bidiyon da aka wallafa a Facebook, YouTube da kuma tallar Google a manyan shafukan yanar gizo a duniya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hazikin Yaro Mai Shekaru 3 Yana Kacaccala Lissafi Ya Birge Jama'a

Bidiyon yarinyar mai matukar taba zuciya mai shekaru tara ya nuna Alexandria tana neman taimako saboda iyayenta na kokarin hada kudin maganinta.

A take, hawaye ke zubowa daga idon yarinyar yana saukowa kan kumatun ta kuma tana sanarwa masu kallo cewa likitoci sun sanar da iyayenta cewa cutar kansa ta karade jikinta.

Alexandria
'Yan Damfara na Amfani da Yarinya Mai Shekaru 9 Wurin Tatsar Miliyoyi Daga Jama'a. Hoto daga Netive Halev
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tallata bidiyon a Facebook, YouTube da Google kuma duk daukar nauyin su aka yi. Bidiyon ya tattara martani a soshiyal midiya kamar yadda binciken Dubawa ya bayyana.

Kamar yadda shafin yanar gizo ya bayyana, kungiyar Netiv Halev dake nemawa yarinyar taimako 'yan damfara ne.

Abinda yasa ake amfani da kansa wurin tsatsar mutane

Rahotanni sun ce kansa tana daya daga cikin cutukan da masana kiwon lafiya ke gwagwarmayar samowa magani. Rahotanni sun nuna cewa cutar tana lamushe rayuka 21,000 a kowacce shekara a duniya.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za a yi zaben 2023 ba tare da wata matsala ba, hafsan tsaro

Don haka, amfani da cutar kansa da yarinya mai shekaru 9 yasa lamarin ya taba zukatan jama'a sosai.

Wallafar ta samu martani 14,000, tsokaci 6500 da sake wallafar 1,900 a Facebook a watan Yulin 2022, kamar yadda Dubawa ta bayyana.

Ta samu martani mai yawa a YouTube, sama da mutumin miliyan 2.9 suka kalla bidiyon.

Jama'a da yawa sun ce sun bada gudumawar sama da $10 inda wata tace gudumawar da ta bada da katinta na asusun daloli yasa an kwashe kudaden dake ciki gaba daya.

Dukkan abun an hada shi ne don damfarar jama'a

An samu gudumawa mai yawa

Domin bada gudumawa, masu bayarwa ana bukatar su saka adireshins na Email, suna, lambar waya kuma a yi amfani da katin banki wurin bayarwa.

Idan aka yi kokarin saka kudin amma ba a yi nasara ba, ana cigaba da tura sako ta Email da su sake gwadawa. Duk wani kokarin da za a yi na duba yunkurin baya, ya kan gagara.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Har a halin yanzu, 'yan damfara suna samu gudumawar $693.199 yayin da suke amfani da kansar bogin Alexandria kuma yawan kudin yanzu ya kai kusan $1.7 miliyan saboda masu damfara na cigaba da samu jama'ar da suke cuta.

Nagode wa Najeriya da ta Bani Ilimi Nagartacce, Mai Arha: Matashin Najeriya Dake Digirin Digirgir a Amurka

A wani labari na daban, wani dalibin Najeriya dake karatun digirinsa na uku a Amurka ya mika sakon godiyarsa gida Najeriya kan gatan da ya samu a fannin ilimi.

Kamar yadda matashin mai suna Ebuka Peter Ezeugwu ya bayyana, da ilimi mai arha kuma nagartacce na Najeriya da ya samu ne yasa har ya iya zuwa kasar waje.

Ebuka a halin yanzu yana karatun digirinsa na uku a fannin injiniyanci a jami'ar Minnesota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel