Obasanjo Ga Marayu A Borno: Ku Yafe Wa Yan Ta'adda Da Suka Kashe Muku Iyaye

Obasanjo Ga Marayu A Borno: Ku Yafe Wa Yan Ta'adda Da Suka Kashe Muku Iyaye

  • Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya bukaci marayu da yan ta'adda suka kashe iyayensu su yafe musu hakan zai sa Allah ya musu sakayya da Alheri a rayuwa
  • Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a 12 ga watan Agusta a lokacin da ya ziyarci makarantar marayu ta 'Future Prowess Islamic School' a Borno
  • Tsohon shugaban kasar ya karfafawa daliban gwiwa su mayar da hankali kan karatunsu don shine abu mafi muhimmanci da za su iya yi a rayuwarsu

Borno - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci yara da ke makarantar marayu a Maiduguri, Jihar Borno, su mayar da hankali kan karatunsu yana mai cewa shine abu mafi muhimmanci da za su iya samu a rayuwa.

Kara karanta wannan

A karo na biyu: Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga ASUU, ya fadi abin da yake so su yi

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a yayin da ya ziyarci 'Future Prowess Islamic School' inda daruruwan yaran da Boko Haram suka kashe iyayensu ke karatu.

Olusegun Obasanjo
Obasanjo Ga Marayu A Borno: Ku Yafe Wa Yan Ta'adda Da Suka Kashe Muku Iyaye. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Tsohon shugaban kasar ya kuma bukaci daliban su yafe wa yan ta'addan da suka halaka iyayensu kuma Allah zai musu sakayya da abu mafi alheri, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Obasanjo ya ce ya ziyarci makarantar shekaru uku da suka gabata kuma ya gamsu da sauye-sauyen da ya gani ya kuma shawarci daliban su dena daukan kansu marayu yana mai cewa 'suna da iyaye a makarantar'

Wani dalibi mai shekara 16, Mustapha Bukar ya yi wa Obasanjo maraba tare da bashi labarin yadda yan ta'adda suka kashe iyayensa a gabansa.

Dalibin ya ce lokacin yana da shekara bakwai bayan sun kammala sallar asuba sai suka ji karar harbin bindiga, suka garzaya dakin mahaifinsu tare da shi.

Kara karanta wannan

Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa

"Munyi zaton sojoji ne, yan mintuna wasu mutane suka shigo gidanmu suka ce iyayen mu su tsaya mu kuma mu fita. Muna shirin fita kawai muka ji harbin bindiga. Da muka juya, sun kashe mahaifan mu."

Labarin Bukar daya ne cikin miyagun abubuwan da yan ta'adda suka yi wa yaran Borno kuma akwai yara irinsa da dama a makarantar.

Martanin Obasanjo

Obasanjo ya ce labarin Bukar ya sosa masa zuciya amma ya tabbatar masa makarantar zai dauke masa kewa yana mai cewa yanzu yana da iyaye a makatantar kuma zai cigaba da tallafa musu.

"Abin da ya kamata ka tuna shine wadanda suka zo suka kashe iyayen ka sunyi iya abin da za su iya amma don Allah ka yafe musu. Ka yafe musu kuma Allah zai saka maka da abu mafi alheri," Obasanjo ya fada wa Bukar.

Jawabin mai makarantar

Barrista Zanna Mustapha ta gode wa Obasanjo kan ziyarar da ya ke kawo wa lokaci zuwa lokaci wanda hakan yasa wasu manyan mutane ke taimaka wa makarantar.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya Shaidawa ‘Yanuwan Fasinjojin Jirgin da Aka Dauke Ya Bayyana

Obasanjo: A Duba Kwakwalwar Duk Wanda Ya Ce Abubuwa Na Tafiya Dai-Dai A Najeriya

A wani rahoton, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya bata kai matsayin da ya kamata a ce ta kai ba.

A cewar Obasanjo, duk wanda ya ce abubuwa suna tafiya dai dai a kasar na bukatan a duba kwakwalwarsa, The Cable ta rahoto.

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba wurin lakca na shekara-shekara ta Gidauniyar Badejo a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164