Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa

Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa

  • Wani dan Najeriya, Black Nells, ya jinjinawa kyakkyawar masoyiyarsa wacce bata taba yanke kauna da shi ba
  • Matashin ya wallafa bidiyon sauyawar da suka yi a TikTok don nunawa masoyansa yadda Allah ya tarbawa garinsu nono
  • Nells ya tuna yadda kawayen matarsa suka dunga bata shawara a kan ta rabu da shi amma ta ki bin shawararsu

Najeriya - Black Nells ya karfafawa mazajen da suka yanke kauna da samun soyayya ta gaskiya saboda talauci da ya masu katutu gwiwa a TikTok.

Yayin da yawanci matan yanzu ke neman ‘manyan Alazawa da suka ci suka tada wuya’, Nells ya bayar da labarin sauyin da ya samu don tabbatar da cewar har yanzu ana iya samun mata da ke tsayawa tsayin daka da mutum har zuwa lokacin da zai yi nasara a rayuwa.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya

Nells ya hadu da masoyiyarsa wasu yan shekaru da suka gabata lokacin da gari ya yi masa zafi. A cewarsa, ya kasance talaka kuma mummuna a wancan lokacin.

Masoya
Tare Da Ita Muka Sha Gwagwarmayar Rayuwa: Bidiyon Yadda Magidanci Ya Canza Rayuwar Matarsa Hoto: @blacknellsl
Asali: UGC

Duba ga talaucinsa, sai kawayen budurwarsa suka shawarceta a kan ta rabu da shi sannan ta nemi mai kudi, amma sai budurwar ta ki amsa tayinsu. Tana matukar sonsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nells ya zama mai hali, yana kashewa masoyiyar tasa kudi

Koda dai Nells bai bayyana irin sana’ar da ya kama ba, yanayin sauyawarsa a bidiyon ya nuna cewa lallai ya tara kudi a yanzu.

Bidiyon sauyin da ya samu ya nuno su suna saukowa daga wata hadaddiyar mota tare da masu tsaronsu tsaye a gefensu.

Yanayin adon da suke yi ya sauya ba kadan ba sannan kamanninsu ya canja gaba day aba kamar lokacin da suka hadu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

Matar tasa ta kara kyau sosai kuma mutane sun yaba da yadda yake kashewa matar tasa kudi da fito da ainahin kyawunta.

Da yake yada bidiyon a TikTok, Nells ya ce:

“A makaranta, ana yi mata ba’a a kan soyayya da mummuna kuma talaka iri na. amma bata yanke kauna da ni ba. Mun sha yunwa kuma mun koka a tare. Duhu ya yaye sarauniyata."

Jama’a sun yi martani a kan bidiyon

@tberry34 ta ce:

“Saboda ka yaba da abun da ta yi na kasancewa tare da kai a lokacin da baka da komai, kuma na ga mutuncinka a kan haka, Allah ya ci gaba da buda maka.”

@breeze__aj ya ce:

“Baaba sun barni kuma har yau ban ga komai ba. Na kalli wannan soyayyar amma yana nan yadda yake. Za mu ci gaba da rayuwa.”

@mhizbecky4 ta ce:

“Baaba na ji dadi ka tuna da ita fa abu ne mai kyau Allah ya albarkace ka a kan haka.”

Kara karanta wannan

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

@shugabby4 ta ce:

"Wannan abu ya yi dadi sosai tunda baka taba manta yadda kuka fara ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin kuma, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin hotunan yadda wata matashiya ta sauya gaba daya bayan ta yi aure da sahibinta.

Matar mai suna Juliet ta je shafinta na TikTok don wallafa wani tsohon hotonta don nuna yadda kamanninta suke a lokacin da take sabuwar amarya.

Fatar jikin Juliet na da dan duhu kuma bata da jiki a hoton. Sai dai kuma, sabon hotonta ya nuna yadda ta sauya gaba daya ta kara wani irin kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng