A Karo Na Biyu, Shugaba Buhari Ya Sake Rokon ASUU Su Yi Hakuri Su Janye Yajin Aiki

A Karo Na Biyu, Shugaba Buhari Ya Sake Rokon ASUU Su Yi Hakuri Su Janye Yajin Aiki

  • Jamia'ar Maidguri ta karrama Alhaji Muhammadu Indimi a wani kasaitaccen biki da aka shirya a jihar
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar ASUU ta gaggauta janye yajin aikin da take yi a yanzu
  • Kungiyar malaman jami'a a Najeriya sun shafe akalla watanni bakwai suna yajin aiki saboda wasu bukata da ta gabatarwa gwamnati

Maiduguri, jihar Borno - Yayin da kungiyar malaman jami'o'i suka shafe akalla watanni bakwai suna yaji, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci su hakura su janye yajin.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, Buhari ya bayyana hakan ne a taron bikin karrama Alhaji Muhammadu Indimi, shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Ltd a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An gudanar da wannan babban taro ne a cikin jami'ar Maiduguri, daya daga cikin manyan makarantun Najeriya da ke garkame sakamakon yajin ASUU.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga kungiyar ASUU
A Karo Na Biyu, Shugaba Buhari Ya Sake Rokon ASUU Su Yi Hakuri Su Janye Yajin Aiki | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa Alhaji Ibrahim Gambari, wanda ya zanta kan batutuwa da yawa da suka shafi ilimi a Najeriya, The Nation ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake tuna batun ASUU tare da yin tsokaci a kai, Gambari ya isar da sakon Buhari da cewa:

“Yana da kyau mu ce wani abu game da wannan yajin aikin na ASUU saboda muna karrama Alhaji Indimi wanda aka shirya wa gagarumin biki a yau domin ci gaban ilimi mai inganci da ya kawo ba a kasar nan kadai ba.
"A kan haka, ina so in isar da kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari game da ASUU da ta janye yajin aikin da take yi, ta koma aiki".

Tattaunawa da ASUU ta yi nisa, in ji Buhari

A bangare guda, Buhari ya ce tuni tattaunawa tsakanin ASUU da gwamnati, amma duk da haka kungiyar ta ci gaba da bude makarantu.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Hakazalika, ya kuma koka da cewa, bai dace ASUU su ci gaba da ajiye dalibai a gida ba kasancewar abubuwa sun ksa kankama.

A cewarsa, irin wannan tsawaita wa’adin yaji na dakushe ilimi tare da kawo cikas ga ci gaban al’umma, Guardian ta ruwaito.

Buhari ya fusata, ya ba ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin ASUU

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware matsalar yajin aikin da kungiyoyin ma'aikatan jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makwanni biyu, Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi wasu bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin na jami’o’i da gwamnati.

Kun ji cewa, ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran kungiyoyi su ma suka tsunduma bayan ganin rashin daidaiton sakamako da gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu.

Kara karanta wannan

Nagode wa Najeriya da ta Bani Ilimi Nagartacce, Mai Arha: Matashin Najeriya Dake Digirin Digirgir a Amurka

Asali: Legit.ng

Online view pixel