Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije

Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije

  • A makon nan ne diyar tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigon jam'iyyar PDP, Sule Lamido, Surayya Lamido zata shiga daga ciki
  • Za ta auri Turakin Zamfara kuma kwamishinan kasuwanci na jihar mai ci, Yazid Shehu Fulani
  • Tuni bidiyo da hotunan shagalin bikin wanda aka fara suka yadu a shafukan soshiyal midiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - A cikin wannan makon ne diyar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Surayya Sule Lamido za ta shiga daga ciki.

Surayya za a ta auri kyakkyawan angonta wanda ya kasance kwamishinan kasuwanci na jihar Zamfara, Yazid Shehu Fulani.

Surayya da Yazid
Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Tuni dai aka fara gudanar da shagalin wannan biki inda aka shirya kasaitaccen liyafar sa lalle wanda ya samu halartan amarya da kawayenta.

A cikin bidiyon liyafar wanda ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amarya a filin rawa tare kawayenta suna girgijewa.

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan, jama’a sun taru ana ta yi mata likin kudade yayin da take rera wakar nan yar yayi ta turanci wato ‘Buga’.

Kalli bidiyo da hotunan a kasa:

Hotuna: Tsantsar Kyawun Wani Ango Da Amaryarsa Ya Sa Mutane Yamutsa Gashin Baki A Soshiyal Midiya

A wani labarin, a karshen makon jiya ne aka daura auren wani kyakkyawan ango mai suna Abdul’ziz Babaji da hadaddiyar amaryarsa Aisha Aliyu Othman.

Hotunan ma’auratan ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda suka yi shigarsu ta sabbin aure mai cike da kamala.

Sai dai tsantsar kyawu da suke da shi shine abun da ya fi jan hankalin mabiya shafukan soshiyal midiya, harma wasu na hango yadda zuri’ar da za su samu a gaba za su kasance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel