Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa

Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa

  • Kyawawan hotunan dalleliyar amaryar Kabiru Aminu Ado Bayero, Aisha Ummarun Kwabo, sun bayyana kuam sun matukar kayatarwa
  • A hotunan kafin biki da katin daurin auren da ya fito, an ga angon sanye cikin kayan sarauta yayin da zukekiyar amaryarsa ta yi shigar alfarma
  • Za a daura auren a jihar Sokoto a ranar Juma'a, 26 ga watan Augustan 2022 da misalin karfe biyu na rana

Kano - Birnin Sokoto zai dauka manyan baki inda ake sa ran zai cika dankam da jama'ar da zasu halarci daurin auren 'dan Sarkin kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, Kabiru Aminu Bayero da dalleliyar amaryarsa Aisha Ummarun Kwabo.

Tuni dai shirin wannan bikin na 'yan gata ya kankama inda har aka yi hotunan kafin bikin na amarya da ango cike da izza tare da bayyanar al'adun sarauta.

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

Prince Kabiru Bayero
Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

A hotunan da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga jinin sarauta tare da zukekiyar amaryarsa sun cakare gwanin sha'awa.

Kamar yadda katin bikin ya bayyana, za daura auren a ranar Juma'a, 26 ga watan Augsutan 2022 da karfe 2 na rana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Iyalan mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da na Alhaji Ummarun Kwabo A.A MFR Jarman Sokoto, suna farin cikin gayyatar ku zuwa daurin auren ya'yansu
"Kabiru Aminu Ado Bayero da Aisha Ummarun Kwabo wanda za a yi a:
"Wuri: Lamba daya Polo Club Gwiwa Area, Jihar Sokoto.
"Rana: 26 ga watan Augustan 2022 da karfe 2 na rana," katin yace.

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

A wani labari na daban, wani fusattacen dattijo ya yi wa wani matashi tatas tare da budurwar da ya gani suna tadi a mota, cikin duhu kuma a lungu.

Kara karanta wannan

Auren Sarauta: Dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa

Kamar yadda dattijon ya bayyanawa matashin hakan bai dace ba a addinance kuma sabawa hanyar neman aure ce kai tsaye, kamar yadda @northern_blog ta wallafa.

Bidiyon da har yanzu Legit.ng bata san a inda aka nade shi ba, ya bayyana cike da duhu, ba a ganin fuskar saurayin balle budurwar saboda alamu na nuna da dare ne lamarin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel