Bankin Duniya Ya Lissafa Kasashen Afirka 34 da Ke da Tarin Bashi Kuma Ka Iya Samun Yafiya

Bankin Duniya Ya Lissafa Kasashen Afirka 34 da Ke da Tarin Bashi Kuma Ka Iya Samun Yafiya

 • Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) sun saki jerin sunayen kasashen duniya da ke da dimbin basussuka akansu
 • A cewarsu, kasashe 39 da ke cikin jerin, 34 na Afirka ne kuma sun cancanci a yafe wasu wadannan basussuka
 • Hakazalika, jerin ya bayyana ka'idojoji da sharuddan da kasashen za su bi wajen saryar da wannan bashi mai yawa

A cewar wani rahoton Business Insider, akwai kasashe matsakata karfi 34 a Afirka da ke da dimbin basussuka akansu.

Jerin ya fito ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa na Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

An dai kaddamar da shirin ne a 1996. Bayanai daga asusun IMF na cewa, shirin na son tabbatar da cewa babu wata kasa matsakaiciya da za ta fuskanci nauyin bashin da ba za ta iya sarrafa kanta ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

Kasashen Afrika masu tarin bashi
Bankin Duniya Ya Lissafa Kasashen Afirka 34 da Ke da Tarin Bashi Kuma Ka Iya Samun Yafiya | Hoto: Jasmin Merdan
Asali: Getty Images

Kasashe 39 a duniya da suka shiga jerin sunayen IMF da Bankin Duniya

Yunkurin yafe basussukan yana aiki ne ta hanyar kungiyoyin kudi da yawa ciki har da masu ba da lamuni na duniya kuma suna hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen ne don rage basussukan waje zuwa matakan da za a iya sarrafawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin kasashe 39 da ke cikin jerin, 34 kasashe ne na Afirka kuma suna da adadin mutane kusan miliyan 760 a jumillance.

Kasancewarsu kasashen da aka ce suna fama da fatara ba shine ma'aunin shiga jerin kasashe masu fama da bashi mai yawa ba. Sauran sharuddan sun hada da ingantaccen tarihin iya yakar fatara.

Lissafin IMF ya nuna cewa dole ne kasashe su cancanci karbar lamuni daga Hukumar Raya Kasashe ta Bankin Duniya.

Ga dai jerin kasashen kamar haka

 1. Ghana
 2. Tanzaniya
 3. Habasha
 4. Benin
 5. Burkina Faso
 6. Burundi
 7. Kamaru
 8. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
 9. Chadi
 10. Tsibirin Comoros
 11. Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
 12. Jamhuriyar Kongo
 13. Ivory Coast
 14. Eritrea
 15. Habasha
 16. Gambiya
 17. Gini
 18. Guinea-Bissau
 19. Laberiya
 20. Madagascar
 21. Malawi
 22. Mali
 23. Mauritania
 24. Mozambique
 25. Nijar
 26. Rwanda
 27. Sao Tome da Principe
 28. Senegal
 29. Saliyo
 30. Somaliya
 31. Sudan
 32. Togo
 33. Uganda
 34. Zambiya

Kara karanta wannan

Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota

A wani labarin, akwai wasu kasashe dake iyaka da Najeriya da mutum zai iya zuwa a mota don yawon bude ido ba tare da hawa jirgi ba.

Tafiya a mota na da amfani matuka saboda mutum zai iya ganewa idonsa abubuwa daban-daban tare da iya daukan hotuna sabanin jirgin sama.

Domin fita daga Najeriya da mota, ana bukatar mutum ya mallaki Fasfot, katin zama dan kasa, da kuma katin shaidan kayi rigakafin zazzabin Yellow Fever, sai kuma isasshen kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel