Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

  • Mista Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party ya yi wa matasa da yan Najeriya albishirin abin da zai iya idan ya ci zaben 2023
  • Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce zai rage talauci da rashin tsaro a kasar ta hanyar samar da ayyuka da bunkasa saka hannun jari
  • A yayin da ya ke jadada muhimmancin hadin kai a kasar, Obi ya kuma ce zai kawo karshen aikata laifi da ake yi da sunan 'tallafin man fetur' a kasar

Dan Takarar Shugaban Kasa na Labour Party, LP, Peter Obi ya jadada cewa zai rage talauci da rashin tsaro idan ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a Najeriya.

Peter Obi.
Peter Obi, Datti Baba-Ahmed, Doyin Okupe a wurin taron matasa na LP. Hoto: @PeterObi.
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya bayyana cewa yana fatan cimma wannan burin ta hanyar samar da ayyukan yi da saka hannun jari. Ya ce zai sauya kasar tattalin arzikin kasar daga mai siyo kayayyaki ta koma mai siyar da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Obi ya bayyana hakan na cikin wasu rubutu da ya yi a sahihin shafinsa na Twitter a ranar Alhamis bayan wani taro da jam'iyyarsa ta shirya da matasan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zan rage talauci da rashin tsaro, sannan zan kawo karshen tallafin mai - Obi

Ya rubuta:

"Bayan mun ci zaben 2023, muna fatan amfani da samar da ayyuka da saka hannun jari don rage talauci da rashin tsaro, mu kuma karkatar tattalin arzikin kasar daga mai siyo kaya zuwa mai sayarwa.
"Babban kalubalen da muke fama da shi bayan rashin shugbanni masu nagarta shine rashin hadin kan manyan kasa. Kada mu manta gargadin Dante Alighieri, na cewa 'an tanadi sashi mafi zafi a wuta ga mutanen da suka ki cewa komai a lokacin da ake fama da fitina.'"

Obi ya kuma ce tarihi na da alaka da daukan mataki, yana cewa dole a dakile rabuwar Najeriya ta hanyar jefa wa shugabanni da suka cancanta kuri'a yayin zabe. Ya kuma ce za a magance kumbiya-kumbiya da ake yi kan tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

"Dole mu rika la'akari da tarihi wurin daukan matakai. An dade ana hasashen rabuwar Najeriya. Shekarar 2023 na da muhimmanci a tarihin mu. Amma kada a bari hakan a faru duk da cewa zabin da masu zabe ke da shi yana da tsauri.
"Ya zama dole mu nemi hanyoyin bunkasa Najeriya baya ga man fetur. Ya zama dole mu kawo karshen wannan aikata laifin da ake kira 'tallafin mai'. Kan yan Najeriya ya rabu saboda addini, kabila da yanki," Obi ya kara.

Tsohon gwamnan wanda aka saba sukarsa cewa ba shi da 'madafa' da zai taimaka masa ya ci zabe ya ce madafarsa shine matasan da ke zaune a wurin taron.

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel