Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya

  • Wasu tsoffin ma’aurata daga Turai sun fada tarkon son junansu har ta kai su ga aure bayan sun hadu a soshiyal midiya
  • Robert Marshall na da shekaru 93, yayin da amaryarsa Anne Cooper ke da shekaru 88, kuma ta ce ta dade tana mafarki da halaye irin na mijin nata tun tana yarinya
  • Sun hadu ne a wani dandamalin kulla soyayya, kasancewar su dukka zaurawa ne, kuma mutumin ya bayyana cewa yana ganinta ya fada tarkon sonta

Wata amarya da angonta sun tabbatar da wannan fadin da ake na cewa soyayya na sama da komai yayin da suka kulla auratayya a tsakaninsu duk da tsufansu.

Masoya
Yadda Tsoho Dan Shekara 93 Ya Angwance Da Budurwarsa Mai Shekaru 88, Sun Hadu Ne A Soshiyal Midiya Hoto: PEOPLE
Asali: UGC

Tsoffin ma’auratan basu yanke kauna da samun soyayya ta gaskiya ba

Babu abun da ya kai samun abokin rayuwa, wanda zuciyarka ke shaukinsa tare da burin son kasancewa da shi muddin rayuwarka.

Wasu tsoffin masoya sun auri junansu, kuma sun bayyana cewa sun hadu da soyayya a daidai lokacin da basu yi tsammanin samunsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su dukkansu zaurawa ne lokacin da suka yanke shawarar shiga wata dandamalin kulla soyayya da baiwa tsoffin damar samun masoya.

Robert na a cikin dandamalin kulla soyayyar lokacin da ya ci karo da hoton matarsa sannan ya ce sai ya ji wani abu ya caki zuciyarsa game da hoton kuma ya ji a ransa cewa ita din tasa ce.

A cewar PEOPLE, Anne ta bayyana cewa farkon haduwarsu da Robert ya kwantar da kansa sosai kuma tun daga yadda ya gabatar da kansa ta san cewa ta fada tarkon soyayya.

Karara ya nuna masoyan sun damu da junansu yayin da suka yada hotunan junansu cike da shauki.

Ma’aurata Sun Maka Makwabcinsu Da Zakaransa A Kotu, Hotunan Sun Yadu

A wani labarin, wani dattijon kasar Jamus, Friedrich-Wilhelm K. da matarsa, Jutta sun maka makwabcinsu a kotu saboda hayaniya.

Friedrich ya ce makwabcinsu na da wani zakara, Magda, wanda suka yi ikirarin cewa yana cara sau 200 a rana; lamarin da suka bayyana a matsayin ‘azabtarwa’.

Ma’auratan sun fara shirye-shiryen kai mai Magda, Michael, gaban kotun yankin kan caran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel