Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota

Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota

Akwai wasu kasashe dake iyaka da Najeriya da mutum zai iya zuwa a mota don yawon bude ido ba tare da hawa jirgi ba.

Tafiya a mota na da amfani matuka saboda mutum zai iya ganewa idonsa abubuwa daban-daban tare da iya daukan hotuna sabanin jirgin sama.

Domin fita daga Najeriya da mota, ana bukatar mutum ya mallaki Fasfot, katin zama dan kasa, da kuma katin shaidan kayi rigakafin zazzabin Yellow Fever, sai kuma isasshen kudi.

Ga jerin wasu kasashen Afrika da dan Najeriya zai iya ziyarta a mota:

1. Kasar Ghana

Mutum zai iya bin shata idan suna da yawa ko kuma ya shiga motar haya daga Jibowu ko Maza-Maza a Legas zuwa birnin Accra ko Weija a Ghana.

Ka tabbatar ka yi tanadi kudin Ghana wato Cedis.

2. Kasar Togo

Za ka iya zuwa Togo tare da motocin kamfani ko kuma ka shiga Bas a tashar Mile 2 a Legas.

3. Kasar Mali

Mutum zai iya bin shahrarriyar hanyar Katsina-Maradi duk da cewa akwai kalubale. Hakazalika mutum zai iya zuwa Togo sannan ya shiga motar Mali.

KU KARANTA: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger

Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota
Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotun Koli ta tabbatar da soke jam'iyyun siyasa 74

4. Kasar Kamaru

Za ka iya shiga Kamaru ta kudancin Najeriya. Da birnin Calabar a jihar Cross River, za ka je garin Ekon, sannan ka isa iyakar Kamaru. Za ka iya shiga motar Bas daga Ekom zuwa Douala.

5. Kasar Ivory Coast

Kasar Ivory Coast, ko Côte d’Ivoire na yammacin Afrika. Za ka iya zuwa Ivory Coast ta Maza-Maza a jihar Legas.

6. Kasar Benin

Za ka shiga mota a tashar Mile 2 a Legas zuwa Seme. Sannan ka shiga motar Tasi zuwa Kotono.

7. Kasar SierraLeone

Za ka iya shiga mota a tashar Mile 2 a Legas. Hakazalika zaka iya shiga kwale-kwale, kamar yadda yan wasan Super Eagles suka yi kwanaki.

A bangare guda, mun kawo muku jerin shugabannin kasashen Afrika mafi daukan Albashi.

A cewar Answer Afrca, shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ne shugaban kasa a Afrika mafi yawan albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel