Kun Taimaki Gwamnati a Lokacin Korona, to Ku Taimaki ASUU a Yanzu, Lauya Ya Roki Dangote da Otedola

Kun Taimaki Gwamnati a Lokacin Korona, to Ku Taimaki ASUU a Yanzu, Lauya Ya Roki Dangote da Otedola

  • Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) dai ta shiga yajin aikin tun a watan Fabrairu, inda ta bukaci a kara samar da kudade ga tsarin jami’o’in da kuma karin albashi ga mambobinta
  • Aiwatar da yarjejeniyar da aka tattaunawa da gwamnatin Najeriya a shekarar 2009 na daga cikin abubuwan da kungiyar ta ASUU ta bukata
  • Wani ma’aikacin shari’a ya roki attajiran Najeriya da su sa baki, yana mai cewa gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar magance matsalar

Najeriya - Wani lauya, Pelumi Olajengbesi, ya roki manyan shugabannin bankuna da ’yan kasuwa attajirai da suka hada da Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdul Samad Rabiu, da Mike Adenuga da su lale Naira tiriliyan 1.1 domin biya ma ASUU bukatunsu.

Lauyan ya ce gwamnatin tarayya ta nuna halin ko in kula da kuma nuna rashin damuwa wajen warware yajin aikin ASUU da ya fara tun ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Kara karanta wannan

Harin Cocin Owo : MURIC ta Bukaci Gwamnan Ondo ya Biya Fulani Diyya Tunda Gaskiya Ta Fito

An nemi attajiran Najeriya su kawo karshen aikin ASUU
Kun Taimaki Gwamnati a Lokacin Korona, to Ku Taimaki ASUU a Yanzu, Lauya Ya Roki Dangote da Otedola | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Don haka, ya bukaci ‘yan kasuwar da su tashi tsaye a yanzu kamar yadda suka yi a lokacin annobar Korona, lokacin da suka ba da gudunmawar kudade ga gwamnatin Buhari.

A wata sanarwa da Legit.ng ta samo, lauyan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“’Yan Najeriya masu kishin kasa za su iya kira ne ga manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdul Samad Rabiu, Mike Adenuga, da shugabannin bankuna da su kawo dauki ga talakawan Najeriya da ‘ya’yansu da ba sa zuwa makaranta na tsawon watanni bakwai a wannan shekara."

'Yan Najeriya da dama sun sha yin tsokaci game da wannan batu na ASUU, inda wasu ke cewa, ko da bashi ne ya kamata gwamnatin Buhari ta nemo shi domin dinke barakar zaman banza ta dalibai.

Korona: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka baya

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan yan Najeriya da kungiyoyi da suka tashi tsaye wajen yaki da annobar Korona wacce aka fi sani da coronavirus.

Shugaban kasar a wani jawabi daga kakakinsa, Mista Femi Adesina a Abuja a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ya jinjinawa wa mambobin hukumomi masu zaman kansu a Najeriya kan hada kai da suka yi wajen yakar cutar ta Korona.

Ya yaba ma mutane kamar haka, Dangote, Abdulsamad Rabiu na gidauniyar BUA, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Jim Ovia na UBA, bankunan Access, GTB, Zenith kan gudunmawar naira biliyan daddaya da kowannensu ya bayar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel