Da Duminsa: Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60

Da Duminsa: Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60

  • Kungiyar malaman kwalejojin Ilimi na Najeriya, COEASU ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kimanin watanni biyu tana yi
  • Dr Ahmed Lawan., Sakataren Kungiyar COEASU na kasa ne ya bayyana da hakan cikin wata ta sanarwa da ya fitar bayan taron NEC na kungiyar
  • Malaman na kwalejojin Ilimi sun ce za su bawa gwamnatin tarayya kwanaki 60 domin ganin yadda za a aiwatar da alkawurran da aka musu sannan su san mataki na gaba

Lakcarorin Najeriya karkashin kungiyar malaman kwalejojin ilimi, COEASU, sun janye yajin aikin da suka yi na tsawon kwanaki 60, The Punch ta rahoto.

An dauki wannan matakin ne a babban taron shugabannin kungiyar na kasa da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

A karo na biyu: Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga ASUU, ya fadi abin da yake so su yi

Tambarin COEASU
Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Punch ta rahoto COEASU ta fara yajin aikin ne a ranar 10 ga watan Yunin 2022 a wani yunkuri na ganin an biya mata bukatunta da kawo karshen kallubalen da ke fuskantar kwalejin ilimi a kasar.

Kamar takwarorinsu na jami'o'i, wato ASUU, COEASU ta bukaci gwamnatin ta rungumi tsarin biyan albashi na UTAS.

"Yayin da ta ke godewa masu ruwa da tsaki bisa rawar da suka taka wurin janye yajin aikin, bisa la'akari da nasarori da cigaba da aka samu yayin tattaunawa da kokarin yin garambawul ga dokar kwalejojin ilimi wanda ke da muhimmanci ga tsarin na COE.
"NEC ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin kasa baki daya da ta fara a ranar 10 ga watan Yunin 2022 na tsawon kwana 60 don bawa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da suka cimma da kungiyar bayan hakan NEC za ta sake zama don duba matsayin batutuwan da suka gabatarwa don daukan mataki na gaba," in ji kungiyar cikin sanarwa mai dauke da sa hannun sakatarenta, Dr Ahmed Lawan.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Kawo yanzu, kungiyar malaman jami'o'i ne kawai har yanzu ba su janye yajin aikin ba.

Yajin Aikin ASUU: Yanzu Dankali Na Ke Sayarwa, In Ji Lakcaran Jami'ar Najeriya

A wani rahoton, Christiana Pam, wata lakcara a Jami'ar Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta ce sana'ar sayar da dankali ta runguma domin kula da kanta tun bayan fara yajin aikin ASUU.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta fara yajin aikin gargadi na sati hudu. Kungiyar ta tsawaita yajin aikin da watanni biyu a ranar 14 ga watan Maris don bawa gwamnati daman biya musu bukatunsu. Ta sake tsawaitawa da sati 12 a ranar 9 ga watan Mayu.

A makon da ta gabata ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da wata daya, ta sha alwashin ba za ta janye ba sai an biya mata bukatunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel