Harin Cocin Owo: MURIC Ta Nemi Biyan Diyya Ga Fulani Da Aka Kaiwa Hari

Harin Cocin Owo: MURIC Ta Nemi Biyan Diyya Ga Fulani Da Aka Kaiwa Hari

  • Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Musulunci MURIC ta bukaci gwamnan jihar Ondo ya biya Fulanin da aka kai wa hari a garin Owo diyya tunda gaskiya ta fito
  • MURIC tayi kira ga 'yan Najeriya da su daina yanke hukunci ba tare da samun wani shaida ba dan kiyayyar da ake dashi ga wani kabila
  • Kungiyar MURIC ta jinjinawa jam'ian tsaro bisa nasarar da suka samu wajen kama wadanda suka kai hari cocin Owo

Jihar Ondo - Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Musulunci MURIC, a ranar Alhamis ta yi kira da a biya diyya ga Fulanin da aka yi ramuwar gayya akan su bayan harin da aka kai wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Owo a Jihar Ondo.Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

Legit.NG ta rawaito labarin yadda matasa suka kaiwa Fulani mazaunan garin Owo hari bisa zargin su suka kashe masu ibada cocin St. Francis.

Sai dai rundunar sojin Najeriya a ranar Talata ta ce an kama wadanda ake zargi da kai harin tare da bayyana sunayen wadanda ake zargin yan Ebira ne daga Okene a jihar Kogi.

MURIC
Harin Cocin Owo: MURIC Ta Nemi Biyan Diyya Ga Fulani Da Aka Kaiwa Hari FOTO Gazette
Asali: UGC

MURIC, a cikin wata sanarwa da daraktan ta, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a jiya, Alhamis, ya bukaci gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da ya biya diyya ga Fulanin da aka kashe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ya cigaba da cewa a biya wadanda suka yi asarar dukiyar su diyya kuma a samar da wani nau'i na agaji ga iyalan wadanda aka kashe a cikinsu.

MURIC ta yi kira ga 'yan Najeriya da su daina yanke hukunci ba tare da kwakwarar shaida ba dan kiyayyar da ake dashi ga wani kabila.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Ba yadda za a yi Buhari ya ci bashin N1.1tr don biyan bukatun ASUU

Akwai masu laifi a cikin kowani kabila kamar yadda ake samun masu kirki a ko’ina. Kabilu ba sa aikata laifi mutane ne ke aikatawa inji MURIC

Kungiyar ta yabawa jami’an tsaro da kokarin da sukayi wajen bankado wadanda suka kai harin cocin garin Owo.

Dole Kujerar Shugaban Kasa ya Dawo Kudu a 2023 - Akeredolu

A wani labari kuma, Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu yayi ikrarin cewa dole kujerar shugabankasa ya koma yankin Kudu a 2023 saboda kada a saba yarjejeniyar mulkin karba-karba dake tsakanin yankunan kasar. Rahoton PUNCH

Mulkin karba-karba bayan cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana amfani da tsarin tun 1999 da mulki ya dawo hannun farar hula saboda haka bai kamata tsarin ya canza ba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel