Covid-19: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka bayar

Covid-19: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka bayar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan yan Najeriya da kungiyoyi da suka tashi tsaye wajen yaki da annobar Covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

Shugaban kasar a wani jawabi daga kakakinsa, Mista Femi Adesina a Abuja a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ya jinjinawa wa mambobin hukumomi masu zaman kansu a Najeriya kan hada kai da suka yi wajen yakar cutar ta Covid-19.

Ya yaba ma mutane kamar haka, Dangote, Abdulsamad Rabiu na gidauniyar BUA, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Jim Ovia na UBA, bankunan Access, GTB, Zenith kan gudunmawar naira biliyan daddaya da kowannensu ya bayar.

Covid-19: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka bayar
Covid-19: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka bayar
Asali: Depositphotos

Ya kuma yaba masu kan karfafa wa sauran kungiyoyi masu zaman kansugwiwar yin hakan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa bankin UBA ta bayar da naira biliyan 5 ga Najeriya da Afrika, yayinda tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alkawarin naira miliyan 50.

A cewarsa, bankin First Bank na hada hannu da gwamnati, majalisar dinkin duniya da hukumomin fasaha wajen samar da mafita na koyar da akalla yara miliyan daya ta yanar gizo a shirinta na Keep Them Engaged, Keep Them Safe’.

KU KARANTA KUMA: Kasar Iran ta samu karin mutane 144 da suka mutu sakamakon coronavirus, jimlar mutane 2,378 kenan suka mutu

Shugaban kasar ya kuma yaba ma sauran mutanen da suka bayar da gudunmawa, wanda ba lallai ne sun sanar da duniya ba, inda ya ce “Allah ya ga dukkanin abubuwan kuma zai saka ma kowa da alkhairi.”

Ku tuna a baya mun kawo maku cewa a kokarinsa na hada kai domin ganin an ci galaba a kan annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Isiyaka Rabiu ya sanar da kyautar naira biliyan 1 ga gwamnatin tarayya.

Haka zalika, baya ga tallafin tsabar kudi N1,000,000,000 a yanzu haka Abdul Samad ya yi odan karin kayan asibiti da kuma hada da na’urori, injina da kayan gwajin cutar Coronavirus da za’a yi amfani dasu a jahohi guda 9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel