Auren Sarauta: Dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa

Auren Sarauta: Dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa

  • Yariman Kano, Kabiru Aminu Bayero, zai angwance da amaryarsa yar mutan Sokoto, Aisha Ummaran Kwabo
  • Za a daura auren Kabiru da Aisha wacce ta kasance diya ga Jarman Sokoto a ranar Juma'a, 26 ga watan Agusta a jihar Sokoto
  • Tun farko mun ji cewa diyar sarkin Kano itama, Ruqayya Aminu Bayero, za ta shiga daga ciki da angonta Amir Kibiya

Kabiru Aminu Bayero, dan sarkin Kano Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, zai angwance da kyakkyawar amaryarsa.

Yariman ya tsallake jiharsa ta Kano inda ya lula jihar Sokoto wajen zakulo zukekiyar amaryarsa mai suna Aisha Ummaran Kwabo.

Kabiru Aminu Bayero da amaryarsa
Auren Sarauta: Dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero Zai Angwance Da Zukekiyar Amaryarsa Aisha Ummaran Kwabo Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Aisha ta kasance diya a wajen Jarman Sokoto, Alhaji Dr Ummaran Kwabo kuma tuni katin gayyatan auren nasu ya yadu a shafukan soshiyal midiya.

Za a daura auren a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta a yankin Giwa da ke jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Miyagun da Sun fi Karfin ‘Yan bindiga Sun bullo, Kila a Hakura da Zabe a yankin Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun farko dai mun kawo cewa Ruqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, za ta shiga daga ciki.

Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.

“Mace Daya Ba Za Ta Iya Da Wayona Ba”: Dattijo Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Magantu A Bidiyo

A wani labarin kuma, wani dattijo mai shekaru 61 mai suna David Sakayo Kaluhana wanda ke da matan aure 15 da yara 107 ya yi fice kuma ya haddasa cece-kuce a yanar gizo.

A wata da aka yi da shi, David ya fada ma Afrimax cewa akwai yiwuwar zai sake auren wasu matan kuma ya bayyana maza masu mata daya a matsayin marasa wayo.

Kara karanta wannan

Hukumar NECO Ta Ce Zata Fitar Da Sakamakon Jarabwar SSCE Nan Da Kwanaki 45

A cewarsa, tsananin wayo irin nasa ya fi karfin ya auri mace guda daya kuma wannan ne dalilin da yasa ya tara iyali mai yalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel