NECO: Za a Fitar da Sakamakon Jarabwar SSCE Nan da Kwanaki 45

NECO: Za a Fitar da Sakamakon Jarabwar SSCE Nan da Kwanaki 45

  • Rajistaren Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya yi alkawarin fitar da sakamakon Jarrabawar NECO Nan da Kwanaki 45
  • Farfesa Ibrahim Wushishi ya kai ziyarar sa ido a wasu cibiyoyin gudanar da jarabawar NECO a jihar Legas
  • Wushishi ya ce Hukumar NECO ta hada kai da Jam'iyyar Tsaro dan sa ido kan kayar jarabawar da aka tura wuraren dake fuskantar matsalar tsaro

Jihar Legas - Rajistaren Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya yi alkawarin cewa za a fitar da sakamakon Jarrabawar Sakandare ta 2022 (SSCE) nan da kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar karshe. Rahoton Daily Trust

Wushishi ya bayyana haka ne a lokacin da yaje ziyarr sa ido kan yadda jarabawar SSCE ke gudana a wasu cibiyoyi a Legas.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Ana sa ran kammala jarrabawar da aka fara a watan Yuni a ranar 12 ga watan Agusta.

Premium
NECO: Za a Fitar da Sakamakon Jarabwar SSCE Nan da Kwanaki 45 FOTO Premium Times
Asali: UGC

Wushishi yace suna kan lamarin kuma suna ba da tabbacin cewa za a fitar da sakamakon jarabawar da ke gudana nan da kwanaki 45 bayan kammala na karshe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa dalibai 1.29m suke zana jarabawar da ake yi.

Da yake tsokaci kan rashin tsaro a wasu sassan kasar, shugaban NECO ya bayyana cewa an yi isassun shirye-shirye da jami’an tsaro don sa ido akan kayan jarabawar.

Buhari, Tinubu, IGP, Oyetola, Da Sauran Su Sun yi Jimamin Mutuwar Tafa Balogun

A wani labari kuma, A jiya ne shugaba Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga rundunar yan sandan Najeriya, yan uwa da abokan arziki na tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Tafa Balogun da ya rasu a ranar Alhamis. Rahoton The Nation

Shima dan takarar shugabankasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, Sufeto Janar Usman Baba da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola sun mika na su sakon ta’aziyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel