Jihar Neja: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Kodinetan Hukumar FIRS, Sun Sace Mutum 3

Jihar Neja: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Kodinetan Hukumar FIRS, Sun Sace Mutum 3

  • 'Yan bindiga sun farmaki motar wani kodinetan hukumar haraji ta kasa (FIRS), sun hallaka babban jami'in na gwamnati
  • An sace wasu mutane uku a gidan cin abinci da Saminaka da ke hanyar Lapai-Lambata ta jihar Neja a yankin Arewa maso Yamma
  • Jihar Neja na daya daga cikin jihohin da ke fama da rashin tsaro da hare-haren 'yan ta'adda masu sace mutane

Jihar Neja - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe Kodinetan Hukumar Haraji ta Kasa (FIRS) mai kula da jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi, Alhaji Muhammad Kudu Adamu a daren Lahadi a unguwar Saminaka da ke kan hanyar Lapai-Lambata a jihar Neja.

Wani abokin marigayin mai suna Dokta Zubairu Ibrahim ya shaida wa Daily Trust cewa yana dawowa ne daga garin Lafiagi da ke Jihar Kwara, inda ya je gaishe da ‘yan uwansa da suka dawo daga aikin hajji lokacin da ya gamu da 'yan bindigan.

An sace kodinetan FIRS a jihar Neja
Jihar Neja: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Kodinetan Hukumar FIRS, Sun Sace Mutum 3 | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Ya ce Adamu da wasu mutane uku da ke cikin motar sun yi taho-mu-gama da ‘yan bindigar da suka yi harbin kan mai uwa da wabi ga motarsu, lamarin da ya kai ga rasa rai.

Wasu tanka guda biyu makil da man fetur da aka ajiye a bakin titi suma sun samu harbin bindiga, nan da na suka kama da wuta, inji jaridar This Day.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wajen da lamarin ya faru

Saminaka wani gari ne mai cike da jama'a da ke kan titin Lambata-Bida inda dimbin tankunan mai da manyan motoci da sauran matafiya ke tsayawa don hutun zango.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja (PPRO), DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin, ya kuma ce an yi garkuwa da mutane uku yayin da wasu tankuna biyu suka kama wuta.

Ya ce an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na daren Lahadi.

Abiodun ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan cin abinci a Saminaka inda suka yi awon gaba da mai gidan, Zainab Usman da wasu mutane biyu.

Babban Limamin Saminaka, Alhaji Umaru Mohammed, ya shaida cewa, ‘yan bindigar sun bi wata mata ta kutsa kai cikin masallaci a lokacin da suke karatun Alkur’ani, suka yi awon gaba da ita tare da na'ibin limamin.

Rashin Tsaro: Za a Yi Zaben 2023, Shugaban Tsaro Ya Tabbatarwa 'Yan Najeriya

A wani labarin, yayin da ake ci gaba da ganin tabarbarewar tsaro a kasar nan, babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaben 2023.

‘Yan Najeriya sun nuna damuwar ko za a yi zaben 2023 ganin yadda lamurran tsaro da karuwar hare-haren 'yan ta'adda ke kara ta'azzara.

Sai dai, da yake magana a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a hedkwatar tsaro da ke Abuja, Janar Irabor ya ce sojoji za su yi duk mai yiwuwa don ganin cewa babu abin da ya hana gudanar da zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel