'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba

'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba

  • Miyagun yan bindiga sun hari garin Bali, hedkwatar karamar hukumar Bali a jihar Taraba sun kaashe mutum uku
  • Bayanai sun tabbatar da cewa maharan sun ci karen su babu babbaka a harin na jiya da daddare, sun sace dandazon mutane
  • Wannan harin na zuwa ne a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara lalacewa, Jami'an tsaro sun samu nasara a wasu jihohi

Taraba - Wasu yan bindiga sun kai hari garin Bali, hedkwatar ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba, inda suka kashe mutum uku kuma suka sace wasu da dama ranar Lahadi da daddare.

Wasu majiyoyi da yawa a Bali sun shaida wa wakilin Punch cewa yan bindigan sun farmaki jami'ai a shingen bincike da ke kusa da babban Asibitin garin, daga bisani suka hari mutane.

Harin yan bindiga a Taraba.
'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shugaban ƙabilar Tiv a garin Bali, Zaki David Gbaa (Ter Tiv Bali II), ya bayyana cewa mutanensa biyu sun rasa rayuwarsu, kuma an sace wasu da dama mafi yawa mata a harin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Ango a Katsina

Channels tv ta ruwaito Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maharan sun shigo garin da ƙarfe 11:00 na dare, mutane na biyu sun mutu a harin, wasu biyun kuma sun ji munanan raunuka an kwantar da su a Asibiti. Sun sace mutane da yawa musamman mata."
"Yanayin ya yi muni, ina son kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye kuma su tabbatar da kare rayukan al'umma da dukiyoyin su. Na tsawon awanni huɗu yan bindigan na cikin gari suna harbi kan mai uwa da wabi ba tare da an kawo ɗauki ba."
"Mutane sun fara cire rai da karfin gwamnati wajen kare rayukan su kuma ina tunanin yan fashin dajin nan ba su fi karfin hukumomin tsaron mu ba."

Wane mataakin jami'an tsaro suka ɗauka?

Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin hukumar yan sanda reshen Taraba, Abdullahi Usman, bai cimma gaci ba, kasancewar bai ɗaga kiran salula ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

Amma wani jami'i a hukumar yan sandan jihar ya shaida wa wakilin jaridar cewa mai magana da yawun yan sanda ya halarci wani taro ne game da tsaro.

A wani labarin kuma Sojoji da Yan Banga Sun Yi Wa Sansanin Yan Bindiga Biyu Rubdugu, Sun Kashe Su da Yawa A Arewa

Dakarun Operation Save Haven da haɗin guiwar yan Banga sun samu nasarar ta da sansanin yan bindiga biyu a jihar Filato.

Yayin samamen a yankin ƙaramar hukumar Wasu, jami'an tsaron sun halaka yan ta'adda da dama sun kwato kauyuka biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel