Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Bikin Mutuwa, Suka Sace Masu Zaman Makoki Da Dafaffen Abinci

Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Bikin Mutuwa, Suka Sace Masu Zaman Makoki Da Dafaffen Abinci

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki kauyukan Gidna da Gidan-Dogo da ke jihar Kaduna a yayin da ake tsaka da zaman makokin wani mamaci
  • Maharan sun zauna sun kwashi garar girki da aka yi don bikin mutuwar sannan suka yi guzuri da saura
  • Yan bindigar sun kuma sace mutane da dama da suka halarci wajen makokin kuma akasarinsu mata da baki ne

Kaduna - Al’ummar kauyukan Gidna da Gidan-Dogo da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna sun ce ba za su taba mantawa da ranar da yan bindiga suka farmaki garuruwansu sace mutane da dama.

Kauyukan biyu na a babban titin Bwari-Jere kusa da garin Idah.

A cewarsu, lamarin ya afku ne yan makonni da suka gabata lokacin da mutane daga nesa da kusa suka ziyarci Gidan-Dogo don wani jana’iza, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: 'Yan bindiga sun hallaka Kodinetan hukumar FIRS, sun sace mutum 3

Yan bindiga
Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Bikin Mutuwa, Suka Sace Masu Zaman Makoki Da Dafaffen Abinci Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Gidan-Dogo da ya nemi a sakaya sunansa saboda yanayin tsaro a yankin, ya ce yan bindigar sun farmaki masu zaman makokin da rana tsaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Sun zo da yawansu lokacin da kauyen ya cika da baki wadanda suka zo taron jana’iza. Masu makokin sun dafa tuwo, shinkafa da sauran abinci iri-iri. Yan bindigar sun kwace wadannan abinci da lemukan, suka ci wasu a nan sannan suka tafi da sauran.”

Ya ce yan bindigar sun yi awon gaba da kimanin mutane 40, yawancinsu mata da baki.

Wata yar uwan daya daga cikin wadanda abun ya ritsa da su ta ce lamarin ya tilastawa mazauna kauyukan da dama barin garuruwansu don tsoron ci gaban hare-hare.

Ta ce yan kwanaki bayan harin an saki kimanin mutum 25, amma cewa wasun su sun mutu daga baya saboda halin da suka shiga a daji.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Gida-Gida, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu Da Dama

A cewarta har yanzu akwai akalla mutum 12 a hannun yan bindigar.An tattaro cewa bayan farmakin da yan bindiga suka kai kan sojoji a yankin Bwari da ke birnin tarayya a kwanan nan, sojoji sun kai mamaya sansanonin yan bindiga a yankin Kawu da Ido kusa da garuruwan biyu.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sojoji, kimanin makonni biyu da suka gabata sun zo kauyen a jirgi mai tashi da saukar ungulu don mamayar sansaninsu, inda suka kashe wasun su sannan wasu suka tsere da mutanen da aka sace.

Rahoton ya kuma kawo cewa daraktan labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ya tabbatar da cewat sojoji sun yi nasarar kakkabe kauyukan Kawu da Ido, inda suka kashe yan ta’adda tare da lalata maboyarsu.

Janar Onyeuko, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai na mako kan ayyukan sojoji, ya ce dakarun sun kuma kashe yan ta’adda 30 da suka farmaki sojoji a Bwari.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a Tashan Buja da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 12:30 na tsakar daren Juma’a ba tare da harbi ba sannan suka dauke wata matar aure, danta da wasu mutane shida, jaridar Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel