Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

  • Bidiyon wani ango ya zurfafa a tunani a wajen liyafar aurensa ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya
  • Amaryar dai ta kasance a filin rawa tana rakashewa sai dai sam hankalin mijin ba a kanta yake ba domin ya yi nisa a tunani
  • Mutane da dama na ganin rawar da amaryar ke yi ne ya jefa angon cikin tunanin anya ban shiga 'uku ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Amaren wannan zamani basa iya boye farin cikinsu musamman a wajen shagulgulan bikinsu, inda suke zagewa su shashe da kyau.

Bidiyon wata amarya tana girgijewa yayin da take bin wakar da ke tashi a wajen liyafar bikin ta ya ja hankali a shafukan soshiyal midiya.

Sai dai abun da ya fi jan hankalin mutane shine yadda angon ya zurfafa a cikin tunani yayin da amaryar ke nuna kwarewarta a wajen rawa.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

An dai hasko angon zaune kan kujerar da aka tanada na musamman don su hannunsa a kan kuncinsa wanda ke nuna ya yi zurfi a duniyar tunani.

Amarya da ango
Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu Hoto: LIB
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma gano kawayen amaryar suna kara karfafa mata gwiwa ta hanyar tayata da yin shewa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu

Tuni jama'a suka yi sashin da aka tanada don yin sharhi tsinke inda suka dunga zazzage ra'ayoyinsu kan dalilin da yasa ango shiga tunani.

Khadija Jaafar ta yi martani:

"Ango dai abin duniya ya ishesa,he was like Allah mai iko,ni Kuma abunda na cinko ma kaina kenan."

Amina Aliyu ta ce:

"Tunanin “Anya ban debo ruwan dafa kaina ba”"

Khairat Ibraheem Saleh

"Rawar ya gani, Ya kuma wada yanzu ta kuma barshi da tunanin anya babu matsala"

Umar Kabir Baita ya ce:

"Dukka wannan da sunan wayewa, mun rasa al'adu da martabarmu. Allah ya shiryar damu."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Naaner Queen ta rubuta:

"Ango Kam kaman yaga abun da yafi karfinshi"

Hannatu Farouk Aliyu ta yi martani:

"Cewa yake oh ni na dauko ruwan dafa kaina.....kalli yarda uwargida ke da sanyin hali."

Nafysatu Msk ta ce:

"Alquran ango abun duniya ne ya ishe shi. Tunanin yanda zai zauna da Michael Jackson yake."

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A gefe guda, wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya inda aka gano wani uba yana zubar da hawaye a wajen liyafar bikin diyarsa.

A wani bidiyo da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano mutumin ya rungume diyarsa yayin da su dukka biyun suka fashe da kuka. Daga nan sai wajen ya dauki sowa yayin da su kuma suka tsuma zukata.

An kuma jiyo mai gabatar da shirin taron tana umurtan amaryar da ta fadawa mahaifin nata tana kaunar shi kuma za ta yi kewarsa.

Kara karanta wannan

Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwagwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

Asali: Legit.ng

Online view pixel