Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

  • Wani uba ya tsima zukatan jama’a da suka taru domin taya shi murnar auren diyarsa bayan ya fashe da kuka
  • Kowani mahaifi ya kan cika da farin ciki idan aka ce diyarsa za ta bar karkashinsa zuwa gidanta na aure domin fara sabuwar rayuwa da mijinta
  • A wani bidiyo da ya yadu a Instagram, an gano amaryar da mahaifin nata sun hadu suna kukan murna da kewan juna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya inda aka gano wani uba yana zubar da hawaye a wajen liyafar bikin diyarsa.

A wani bidiyo da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano mutumin ya rungume diyarsa yayin da su dukka biyun suka fashe da kuka. Daga nan sai wajen ya dauki sowa yayin da su kuma suka tsuma zukata.

Kara karanta wannan

Biki ya yi biki: Bidiyon yadda amarya tayi jifa da gwagwaro da takalmi tana cashewa a bikinta

An kuma jiyo mai gabatar da shirin taron tana umurtan amaryar da ta fadawa mahaifin nata tana kaunar shi kuma za ta yi kewarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon Yadda Amarya Ta Dunga Sharban Kuka Wiwi Tare Da Nuna Tirjiya A Wajen Baikonta Ya Haddasa Cece-kuce

A wani labarin, bisa al’ada amare kan kasance cikin farin ciki da annashuwa a duk lokacin da aka ce an taru domin saka ranar aurensu musamman idan aka yi dace da wanda suke burin karasa rayuwarsu da shi ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai lamarin ya sha bamban a bangaren wata amarya da bidiyonta ke yawo a shafukn soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano matashiyar budurwar tana sharban kuka wiwi yayin da take zaune a gefen angonta a lokacin da ake masu baiko.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

Asali: Legit.ng

Online view pixel