Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Mata kan nuna tsananin kishi a duk lokacin da aka ce mazajensu za su kawo masu abokiyar zama
  • Wata uwargida ta nuna jarumta inda ta halarci taron dinan auren mijinta da amaryarsa harma ta sake aka yi komai da ita
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano inda uwargidar ta rungume abokiyar zaman tata harma da sumbatarta a kumatu

Mafi akasari mata kan tayar da hankulansu idan aka ce yau gashi mijinsu zai kara aure, harma su hana zaman lafiya da sukuni a gidan.

Wannan ne babban dalilin da yasa ake yiwa kalmar ‘kishi’ lakabi da kumallon mata. Kuma ma zafin kishi kan sanya wasu matan aikata abubuwan da hankali ba zai dauka ba.

Sai dai a wannan karon, wata uwargida ta sauya wannan labari domin ta yi tattaki ta halarci dinan da aka shiryawa mijinta da amaryarsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Amarya da Uwargida
Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amaryar zaune da angonta a waje na musamman da aka tanada don su. Sai ga uwargida ta iso wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da isowar uwargidar, sai ta rungume mijin nata sannan bata tsaya a nan ba, ta isa wajen amaryar itama ta rungume ta cikin tsantsar so da kauna.

Nan take wajen ya dauki sowa yayin da aka jiyo MC tana yi masu addu’a a kan Allah ya hada kansu ya kuma basu zaman lafiya da juna.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Wannan abu da uwargida ta yi ya haddasa cece-kuce a tsakanin mabiya shafukan soshiyal midiya, yayinda wasu ke ganin jarumtarta wasu sun ce sam hakan bai da wani fa’ida.

attenuerfashionstudio ta yi martani:

“A bari fa…”

rabbatulbaitclothingline ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

“Ameen thuma Ameen ...Amma amryan ta danji shock”

iam_raemuhd ta ce:

“Bai kai zuciya ba ”

sabrs_collection ta rubuta:

“Allah ya bada zaman Lfy ”

saroroh_ ta yi martani:

“Hehehe Allah dan Allah akayi”

addanno_s ta ce:

“ a jira dai”

faab_exquisite_fabrics ta ce:

“Allah ya basu zaman lafiya. ”

badaweescuisine ta ce:

“Yasin bazani event din ba ma balle a fara wani hug”

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A gefe guda, wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya inda aka gano wani uba yana zubar da hawaye a wajen liyafar bikin diyarsa.

A wani bidiyo da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano mutumin ya rungume diyarsa yayin da su dukka biyun suka fashe da kuka. Daga nan sai wajen ya dauki sowa yayin da su kuma suka tsuma zukata.

An kuma jiyo mai gabatar da shirin taron tana umurtan amaryar da ta fadawa mahaifin nata tana kaunar shi kuma za ta yi kewarsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

Asali: Legit.ng

Online view pixel