Budurwa Ta Gane Cewa Mijinta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Da Kafafun 'Acuci' Ya Dinga Zuwa Tadi, Bidiyo

Budurwa Ta Gane Cewa Mijinta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Da Kafafun 'Acuci' Ya Dinga Zuwa Tadi, Bidiyo

  • Wata matashiyar amarya mai suna Bora bata san angonta gurgu bane har sai bayan da aka daura aurensu
  • Bora da mijinta mai suna Joda sun dauki tsawon lokaci suna soyayya amma bai taba sanar da ita kafafun roba bane da shi don gudun kada ta bar shi
  • Koda ta sani bayan aurensu bata watsar da mijin nata ba inda ta rungume shi hannu bibbiyu

Labarin wasu masoya mai taba zukata ya bayyana a shafin soshiyal midiya, inda mijin ya boyewa amaryarsa cewa shi gurgu ne har bayan aurensu.

Mutumin da aka ambata da suna Jado da masoyiyarsa Bora sun shafe tsawon lokaci suna soyayya kafin suka yi aure.

A tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya, Jado ya boyewa Bora cewa bai da kafafuwa saboda tsoron kada ta fasa aurensa.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Miji da mata
Bidiyo: Budurwa ta gane cewa mijinta gurgu ne bayan aurensu, da kafafun 'acuci' ya dinga zuwa tadi Hoto: @CableLifestyle
Asali: Twitter

Hakan ya samo asali ne saboda yadda mata ke rabuwa da shi da zaran sun fahimci nakasar da ke tattare da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Magidancin ya rasa kafafunsa bibbiyu sakamakon tashin bam a lokacin da yake yaro.

Ya hadu da Bora ne a wajen wani gasar waka, inda suka yi musanyar lambobin waya kuma daga nan suka fada soyayya da junansu.

Ita budurwar bata san bai da kafafu ba saboda yana tafiya a kan kafafuwan roba,

A wani bidiyo da ya yadu a shafin soshiyal midiya, budurwar ta ce ta zata wani karaya ne ya sanya baya tafiya da kyau. Amma sai bayan aurensu ne ta gane gaskiyar lamari.

Sai dai kuma, Bora ta ce sam bata yi fushi da mijinta ba bayan ya yi mata bayanin dalilinsa na aikata abun da ya yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

An tattaro cewa yan uwanta sun yi adawa da auren saboda nakasar mutumin. Sai dai duk da haka, bata yarda ta fita daga gidan mijin nata ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Wannan labarin na soyayyarsu ya haifar da martani daga mutane da dama a soshiyal midiya.

@princeOscar111 ya yi martani:

"Soyayya na da kyau❤️"

@Chinnan8 ta ce:

"Maza za su iya wanke kansu kan komai "

@GidiOracle ya ce:

"Awww kuma tana cikin farin ciki"

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A wani labarin, wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya inda aka gano wani uba yana zubar da hawaye a wajen liyafar bikin diyarsa.

A wani bidiyo da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano mutumin ya rungume diyarsa yayin da su dukka biyun suka fashe da kuka. Daga nan sai wajen ya dauki sowa yayin da su kuma suka tsuma zukata.

Kara karanta wannan

Kin Gama Mun Komai a Rayuwa: Lauya Ya Fashe Da Kuka A Gaban Mahaifiyarsa Kan Dawainiyar Da Ta Yi Da Shi

An kuma jiyo mai gabatar da shirin taron tana umurtan amaryar da ta fadawa mahaifin nata tana kaunar shi kuma za ta yi kewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel