Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

  • Fasto Carlton Funderburke ya yadu bayan wa'azin da yayi mai zafi a coci, inda ya yi wa masu bauta tatas kan kasa siya masa agogo mai tsada da suka yi
  • Ya kira masu zuwa cocinsa da matsiyata kuma fatararru kan yadda suka ki karrama shi yadda ya dace, inda yake tambayarsu ko bai cancanci kudin bane
  • Jama'a sun caccaki wannan faston kan mugun son abun duniya da ya nuna a maimakon cika zukatan masu bauta da kalaman Yesu al-Masihu

Wani fasto daga garin Missouri dake Amurka yayi suna bayan bidiyonsa ya bayyana inda yake caccakar masu bauta kan yadda suka gaza siya masa agogon Movado mai matukar tsada.

Fasto da Masu Bauta
Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada. Hoto daga TikTok.KansasCityDefender
Asali: UGC

Fasto ya bukaci masu bauta da su karrama shi

A wa'azinsa, Fasto Carlton Funderburke na cocin Well dake Birnin Kansas, an ji a bidiyo yana sukar mambobin cocin inda yake kiransu da fatararru.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Babu shakka bidiyon ya janyo martani kala-kala a yanar gizo inda wasu ke alakanta shi da zama faston bogi wanda ya fito tatsar kudaden masu zuwa coci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya dauka lokacinsa yana wa'azi kan mabiya su dinga karrama fastoci kuma ya caccaki mabiyansa kan yadda fatararrsu ta kai har ba su iya karrama bukatarsa.

A wallafa wani bangare na wa'azin faston mai zafi ne a TikTok inda aka bar jama'a baki bude suna mamakinsa.

"Bari in rufe kofa sannan in yi magana ga yarana maza da mata masu arha. Kun ga, a haka ne na gane ku matsiyata ne, baku da kudi kuma fatararru ne saboda kun kasa karrama ni. Ban cancanci kudinku bane? Ba zaku iya siya min Louis Vuitton, Prada, St, Johns knit, Red Lobster ko McDonald bane? Ban isa ku siya min Gucci ba?" yace.

Kara karanta wannan

Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya

Faston tun shekarar da ta gabata ya bukaci mabiyansa da su siya masa wani agogo mai tsadaamma suka kasa siya har yanzu.

Daga Tallar Gwanjo Zuwa Miloniya: Bidiyon Matashi Usman Da Allah Yayi wa Daukakar Dare Daya

A wani labari na daban, Usman Ekukoyi, wani 'dan Najeriya dake siyar da gwanjo ya bayyana labarin yadda rayuwarsa ta sauya gaba daya.

A bidiyon da ya fitar a TikTok, Usman ya bayyana yadda ya fara kasuwancinsa da jari kalilan amma Ubangiji ya taimaka masa yanzu ya shahara.

A shekarun da suka gabata, Usman ya saba siyar da kaya a gefen titin jami'ar fasaha tarayya dake Akure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel