Sojoji Sun Kai Farmaki Maɓoyar Yan Ta'adda a Borno, Sun Halaka Dandazon Su

Sojoji Sun Kai Farmaki Maɓoyar Yan Ta'adda a Borno, Sun Halaka Dandazon Su

  • Rundunar Operation Haɗin Kai ta yi nasarar halaka dandazon mayaƙan Boko Haram a wani samame da ta kai sansanin su da ke Gazuwa
  • Wata majiya ta bayyana cewa Soja ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin gwabzawa, yayin da yan ta'adda da yawa suka zama gawa a yankin Bama
  • Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da taɓarɓarewar tsaro ke ƙara muni a wasu sassan Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHƘ) tare da haɗin guiwar Yan Sa'aki (CJTP) sun kashe dandazon yan ta'addan ƙungiyar Jamā’at Ahlis- Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād wacce aka fi sani da Boko Haram.

Leadership ta gano cewa Sojojin runduna ta 21 da ke sansani a Bama, jihar Borno, sun kai samame maɓoyar yan ta'addan da ke ƙauyen Gazuwa, yankin ƙaramar hukumar Bama da safiyar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Shugaban Makarantar Gwamnatin Tarayya A Kaduna, Sun Kashe Rai

Sojojin Najeriya.
Sojoji Sun Kai Farmaki Maɓoyar Yan Ta'adda a Borno, Sun Halaka Dandazon Su Hoto: leadership.ng
Asali: Depositphotos

Yayin samamen, Sojan Najeriya guda ɗaya ya rasa rayuwarsa a lokacin da suke artabu da yan ta'addan.

A wani rahoton sirri da Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi a kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ya tattara, harin ban mamakin ya yi sanadin mutuwar dandazon yan ta'adda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar da jaridar ta samu ta bayyana cewa:

"Mun kashe da yawan su a ƙetaren ruwa. Wasu daga cikin yan ta'addan sun yi yunkurin mai da martanin wuta amma Sojoji suka harbe su har lahira yayin da wasu kuma suka tsere bisa tilas."
"An gano adadi mai yawa na gawarwakin yan ta'addan sun mamaye baki ɗaya wurin. Soja ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin musayar wuta da ƴan ta'addan."

Idan baku manta ba yan ta'addan sun canza wa wurin suna zuwa "Gazuwa ko Markas," daga asalin sunayen wuraren Gabchari, Mantari da Mallum Masari, kuma yana tattare da Mayaka 3,000 da iyalansu na tsagin Abubakar Shekau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IGP ya gayyaci kwamishinonin 'yan sanda a wata ganawa don dinke matsalar tsaro

Yan ta'adda sun kai hari kusa da jami'a

A wani labarin kuma Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kusa Da Wata Babbar Jami'a Najeriya

Tsagerun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kai hari wani yanki da ke kusa da jami'ar fasaha LAUTECH a jihar Oyo.

Bayanai daga yankin sun tabbatar da cewa maharan sun buɗe wuta don tsorata mutane, daga bisani suka tasa mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel