Yanzu-Yanzu: IGP ya Gayyaci Kwamishinonin 'Yan Sanda a Wata Ganawa don Dinke Matsalar Tsaro

Yanzu-Yanzu: IGP ya Gayyaci Kwamishinonin 'Yan Sanda a Wata Ganawa don Dinke Matsalar Tsaro

  • Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya gayyaci dukkan kwamishinonin 'yan sandan kasar domin tattauna batutuwa
  • Majiya ta bayyana cewa, ganawar na da shirin duba lamurran tsaro da mafita a yankuna daban-daban na Najeriya
  • An samu hare-hare a kwanakin baya a Abuja, lamarin da ya kawo cece-kuce a wurin 'yan Najeriya

FCT, Abuja - Yanzu haka dai babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba yana ganawa da daukacin kwamishinonin ‘yan sanda da sauran manyan hafsoshin kasar nan.

An tattaro cewa taron ya biyo bayan karuwar rashin tsaro ne a kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

IGP ya gana da kwamishinonin 'yan sandan Najeriya
Yanzu-Yanzu: IGP ya gayyaci kwamishinonin 'yan sanda a wata ganawa don dinke matsalar tsaro | Hoto: topnaija.ng
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa dabarun dakile wannan rikici su ne kan gaba a cikin manufofin da za a tattauna akai.

Har ila yau, za a tattauna kan daftarin aiki da daidaita ayyukan baburan kasuwanci da masu kafa a fadin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin Tsaro: IGP Ya Umarci a Zagaye Babban Birnin Tarayya Abuja da Tulin Jami’an Tsaro

A wani yunkuri na kawar da fargabar mazauna Abuja dangane da barazanar tsaro da ake gani a baya-bayan nan, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya ba da umarnin tura karin jami’an ‘yan sanda masu yawan gaske zuwa birnin.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an dauki matakin ne domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mazauna, muhimman kadarorin kasa da dai sauran ababe a zagayen birnin tarayya Abuja, rahoton Channels Tv.

IGP ya ba da wannan umarni ne a yayin taron da rundunar ta gudanar a ofishinsa, yayin da yake samun cikakken bayani kan harkokin tsaro a kasar.

Haka kuma ya umarci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da sashen ayyuka, DIG Bala Zama Senchi, da ya sa ido tare da gudanar da umarnin domin tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

Rashin tsaro: FRSC za ta fara kame baburan da ba su da rajista a fadin Najeriya

A wani labarin, a ci gaba da kokarin dakile matsalar rashin tsaro a kasar nan, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta yanke shawarar daukar tsauraran matakai kan baburan da ba su da rajista a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar nan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in kula da harkokin jama’a na hukumar , ACM, Bisi Kazeem, a ranar Litinin, a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Sanarwar ta umurci dukkanin kwamandojin hukumar FRSC 37 da su gaggauta kame duk wani babur da aka gani ba tare da rajista ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel