'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Makarantar Tarayya A Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Makarantar Tarayya A Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kai hari makarantar koyar da ilimin ƙididdiga a ƙaramar hukumar Ƙaura jihar Kaduna da daren jiya Talata
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe mutum ɗaya a harin wanda suka buɗe wuta, sun kuma sace shugaban makarantar da wata mace
  • Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan kashe wani ma'aikacin wucin gadi da ke aikin rabon ragar sauro a yankin

Kaduna - Miyagun yan bindiga sun kai farmaki makarantar koyon ilimin lissafin kididdiga da ke Manchok a ƙaramar hukumar Ƙaura ta jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Yayin harin, yan bindigan sun halaka mutum ɗaya kuma suka yi garkuwa da wasu mutum biyu, cikin su har da shugaban makarantar ranar Talata da daddare.

Harin yan bindiga a Kaduna.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Makarantar Tarayya A Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Daily Trust ta gano cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Talata lokacin da yan ta'addan suka mamaye ƙauyen, kana suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, daga bisani suka tasa mutanen biyu

Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya yi magana bisa sharaɗin boye bayanansa, ya tabbatar da cewa maharan sun kashe mutum ɗaya har lahira.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da wata mace da kuma shugabar makarantar yayin harin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa wannan harin na zuwa ne makonni uku bayan wasu tsageru sun kashe ma'aikacin wucin gadi da ke aikin raba ragar sauro a yankin.

Mai rabon ragar Sauron ya rasa rayuwarsa ne a kan hanyar Zangang-Zankan da ke ƙaramar hukumar da aka kai wannan harin.

Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun hukumar yan sandan reshen jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayar salula da aka jera masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Yan Banga sun kashe Malamin Tsangaya

A wani labarin kuma Yan Bijilanti Sun Halaka Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani a Kano

Yan Banga sun halaka wani Malamin makarantar haddar Alƙur'ani da ake kira Tsangaya a Dabai, ƙaramar hukumar Gwale jihar Kano.

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun hau mutumin da duka ba tare da bincike ba bayan ya tsinci wani jariri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel