Yan Bindiga Sun Kai Hari Kusa da Jami'ar Fasaha LAUTECH a Jihar Oyo, Sun Sace Mutane

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kusa da Jami'ar Fasaha LAUTECH a Jihar Oyo, Sun Sace Mutane

  • Tsagerun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kai hari wani yanki da ke kusa da jami'ar fasaha LAUTECH a jihar Oyo
  • Bayanai daga yankin sun tabbatar da cewa maharan sun buɗe wuta don tsorata mutane, daga bisani suka tasa mutum biyu
  • Har yanzun hukumar yan sanda ba tace uffan ba game da lamarin, amma bayanai sun ce yan sanda sun fara bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Miyagun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kai hari yankin Abaa, wanda ke kusa da jami'ar Fasaha 'Ladoke Akintola University of Technology,' Ogbomoso, sun sace mutum biyu.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa yan bindigan sun mamaye yankin wanda ke karkashin ƙaramar hukumar Surulere a jihar Oyo ranar Alhamis da daddare, sannan suka yi awon gaba da mai Hotel da ma'aikacinsa.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: 'Yan daba sun farmaki coci, sun sace na'urorin buga katin zabe

Taswirar jahar Oyo.
Yan Bindiga Sun Kai Hari Kusa da Jami'ar Fasaha LAUTECH a Jihar Oyo, Sun Sace Mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wasu bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin ma'aikatan jami'ar da ɗalibai na rayuwa a yankin wanda ke gefen babbar hanyar Ogbomoso-Ilorin.

Wani mazauni wanda ya yi magana da sharaɗin ɓoye sunansa ya ce maharan waɗan da yake tsammanin fulani makiyaya ne, sun sace Mamallakin Otal, ma'aikacinsa ɗaya da wani mutum ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa shugaban yankin, Chief John Adepoju, ya sanar da mutanensa su kasance cikin shirin ko ta kwana bayan aukuwar lamarin.

Adepoju ya kira taron mazauna yankin cikin gaggawa domin tattauna batun da kuma matakin da ya dace su ɗauka don kare faruwar hakan a gaba.

Majiyar ta ce:

"Mai Hotel ɗin bai jima da dawowa daga tafiya ba lamarin ya faru. Yan bindigan zasu kai 10 a labarin dana ji daga bakin waɗan da ke wurin, kuma sun buɗe wuta domin firgita mutane, sannan suka yi gaba da mutanen."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: Atiku makaryaci ne, haka ya kalli 'yan Najeriya ya sharara musu karya

"Matsalar da ke faruwa can nesa muna jin labari yau ta zo gare mu kuma abun takaici yanzu ta zama ruwan dare a yankin."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Mai magana da yawun hukumar yan sanda na jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai tabbatar ko musanta faruwar harin ba zuwa yanzu.

Amma Olugbon na Orile Igbon, Oba Francis Alao, ya tabbatar da kai harin, inda ya ce ya tuntuɓi hukumar yan sanda kuma sun faɗa masa tuni suka fara bincike a kai.

Basaraken ya ƙara da cewa mai ba gwamna shawara kan tsaro, Fatai Owoseni, wanda tsohon kwamishinan yan sanda ne, ya na taimaka wa game da lamarin.

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu mayaƙan kungiyar Boko Haram sun kashe kwamandan Yan Bijilanti a jihar Yobe

Yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun shiga har cikin gida, sun kashe kwamandan jami'an tsaron Sa'kai a jihar Yobe.

Bayanai sunyi nuni cewa yan ta'adda sun shiga garin Buni Yadi kuma suka nufi gidan kwamandan kai tsaye suka kashe shi.

Kara karanta wannan

Da ɗuminsa: Ƴan ta'addan Boko Haram sun buɗewa sojoji wuta kusa da Abuja, wasu sun rasa rayukansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel